Abubakar Shekau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abubakar Shekau
Leader of Boko Haram (en) Fassara

30 ga Yuli, 2009 - 20 Mayu 2021
Muhammad Yusuf
Rayuwa
Haihuwa Shekau (en) Fassara, 24 ga Maris, 1973
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Dajin Sambisa, 20 Mayu 2021
Yanayin mutuwa Kisan kai (suicide bombing (en) Fassara)
Karatu
Harsuna Hausa
Larabci
Kanuri
Fillanci
Turanci
Sana'a
Sana'a soja
Aikin soja
Ya faɗaci Rikicin Boko Haram
Tawayen Boko Haram, 2009
Ta'addancin Boko Haram a kamerun
Imani
Addini Musulunci
Rahoto akan barazanar shekau Shugaban Kungiyar boko haram

Abubakar Shekau, an kuma sanshi da Darul Akeem wa Zamunda Tauhid, ko Darul Tauh woto (gidan tauhidi) (larabci دار التوحيد ), an haifeshi tsakanin 1967 ko 1975 (babu tabbaci) dan kabilar Kanuri ne kuma wanda akafi sani da shugaban kungiyar dan ta'addan Boko Haram, suke ikirarin kafa daular Musulunci a yankin Arewacin kasar. Kungiya ce ta masu tayar da bayar baya a Najeriya kamar yadda kasar ta ayyana ta sakamakon fitar da wani faifan bidiyo da Shugaban ta Shekau yayi ya nuna ikirarin kungiyar nayin mubaya'a ga kungiyar dake kokarin kafa daular musulinci a yankin gabas ta tsakiya wato (ISIS). Shekau ya rike matsayin mataimakin shugaban kungiyar a karkashin wanda ya kafa ta Muhammad Yusuf har zuwa lokacin da Yusuf ya rasa rayuwar sa a hannun jami'an tsaron kasar Najeriya a shekara ta dubu biyu da tara, 2009 inda daga bisani ya zama shugaban gungiyar har zuwa yanzu. Abubakar Shekau Musulmi ne kuma mabiyin akidar Sunni Islam ko Salafiyya.[1][2][3][4]

Bayanin Shekau[gyara sashe | gyara masomin]

Asalin yaren haihuwa na Shekau shine Kanuri, amma kuma yana jin harsunan Hausa, Larabci, Filatanci da Turanci sosai. Yayi ikirarin cewa shi Musulmi ne kuma wanda yayi ilimin addinin na Musulunci na ainihi kuma mai bin akidar musulunci sauda kafa.

A faya fayan bidiyon da Shekau yake fitarwa a kafafen Yanar gizo yasha kalubalantar sojojin dake yaki da kungiyar sa cewa yafi karfin su kuma yananan kan agidar sa ta kafa daular Musulunci sannan bazasu iya dakatar dashi ba ko su kasheshi har sai in Allah ne ya kawo karshen rayuwar sa.

A wantan Yuni na 2012 hukumar kasar Amurka ta ayyana Shekau a matsayin dan ta'adda. Tun daga shekarar 2013 ne kasar ta Amurka tayi ikirarin bayar da ladan $7miliyan na dalar Amurka ga duk wanda ya taimaka wajen kama shekau. A wani karin kuma kasar Najeriya ma tayi ikirarin bayar da Naira miliyan 50 ga wanda ya taimaka wajen kama shekau din.

Shekau ya tsallake ma wani harbi da sojojin Najeriya suka yi masa a kafa a samamen da suka kai masa a shekarar 2009. Bayan ya tsallake rijiya da baya ne yaci gaba da kai hare-hare. A daya daga cikin sanannun hare-haren sa akwai wanda yayi garkuwa da yanmatan makarantar sakandare sama da 200 a 2014. Shekau yayi sanarwar cewar ya musuluntar da yanmatan dukkan su daga bisani kuma yayi barazanar yanmatan zasu rinka kai hare-hare kan Kiristoci.

A watan Augusta na sekarar 2016 gungiyar ISIS ta ayyana Abu Musab Al Barnawi a matsayin shugaban gungiyar ta boko haram kuma ya maye gurbin Shekau wanda yaki amincewa da hakan. Saidai daga baya Hukumomin tsaro na kasar ta Najeriya sun kama Albarnawi ranar 26 ga watan Disamba na 2016.

Rayuwar sa ta kashin kai[gyara sashe | gyara masomin]

Shekau dan Najeriya ne kuma yayi ikirarin shi haifaffen kauyen Shekau ne na jahar Yobe. Amma babu tabbaci game da adadin shekarun sa. Ya auri daya daga cikin matan Muhammad Yusuf.

Ana masa lakabi da Darul Tauhid wato Matattarar Kakaita Allah.

Raho tannin rasuwar sa daga bangaren gwamnati[gyara sashe | gyara masomin]

Sau tari bangaren gwamnatin taraiya tasha ikirarin cewar ta kashe Shekau, amma daga bisani sai ya fito a faifan bidiyo ya karyata maganar ta bangaren gwamnatin.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named france24-20120113
  2. "Boko Haram militant leader is dead, Nigerian military says". France 24 (in Turanci). 25 September 2014. Retrieved 19 February 2020.
  3. "Nigeria army claims death of Boko Haram leader". www.aa.com.tr. Retrieved 19 February 2020.
  4. Akinyelure, Didi (27 September 2016). "Dead or alive? The six lives of Boko Haram's leader". BBC News (in Turanci). Retrieved 19 February 2020.