Abubakar Imam

Daga Wikipedia
A tsallaka zuwa: Shawagi, nema

An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin Kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta 'Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen kaga labari mai ma'ana ya sa Dr. R. M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya. A zamansa na Zariya ne Abubakar Imam ya wallafa littafin Magana Jari Ce 1-3, Ikon Allah 1-5 da Tafiya Mabudin Ilimi. Abubakar Imam shi ne editan jaridar Gaskiya Ta fi Kwabo na farko kuma shi ne ma ya rada ma ta sunanta.

[gyarawa] External link

Zaɓaɓɓin kayan aiki
Namespaces

Variants
Actions
Shawagi
Akwatin kayan aiki
A wasu harsuna