Ali Nuhu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukala mai kyau
Ali Nuhu
Rayuwa
Cikakken suna Ali Nuhu Mohammed
Haihuwa Maiduguri, 15 ga Maris, 1974 (50 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Kano
Harshen uwa Hausa
Harshen Waja
Karatu
Makaranta Jami'ar Jos
Matakin karatu Digiri
Bachelor of Arts (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Jarumi, darakta, mai tsara fim da marubin wasannin kwaykwayo
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci
IMDb nm2683171
alinuhu.net
Ali Nuhu
Snapped with the greatest of all time Nigerian movie industry.jpg

ALI NUHU MUHAMAD

An haifi Ali Nuhu a ranar 15 ga watan March a shekarar 1974 a Maiduguri, Jihar Borno, ya girma a jihar Kano, iyayen sa kuma ƴan Balanga ne a jihar Gombe dake arewacin Nigeriya.

Ali Nuhu ba bahaushe kamar yanda wasu ke fada ya fito daga kabilar "WAJA". cikakken sunan mahaifinsa shine "NUHU EMANUEL POLOMA"

Ali ya girma a hannun mahaifiyar sa a jihar Kano bayan sun rabu da mahaifinsa sakamakon bambancin addini, mahaifiyar sa ta rasu a shekarar 1999 shi kuma mahaifinsa ya rasu a shekarar 2020, a halin yanzu Ali Nuhu yana bin addinin Musulunci kamar mahaifiyar sa.

Ali Nuhu jarumi ne, marubuci, mai bada umarni kuma furodusa a masanatar shirya finafinai ta kannywood da Nollywood. Sannan kuma yakan yi rawa a wasu fina-finai.

Ali Nuhu yana finafinan sa cikin harshen Hausa da turanci, sannan kuma yana cikin manyan jarumai da suka kafa masana'antar shirya finafinai ta kannywood.


Shekarun sa 49, ya kuma karanci geography a jami'ar Jos wato "University of Jos" a turance.

Mutane suna masa inkiya da "sarki Ali Nuhu/ King of kannywood, wanda a ƙalla zuwa yanzu ya fito a finafina sama da 500+ wanda ya samu lambobin yabo da dama. ko a wannan shekara saida ya samu lambar yabon "best actor award in the Nollywood Europe Golden Award (NEGA 2023)".

Ya fara harkar finafinai tun a shekarar 1999 wato shekarar da mahaifiyar sa ta rasu da wani fim mai taken "ABIN SIRRI NE" ya kuma fito a finafinan masana'antar shirya finafinai ta kudancin Nigeria NOLLYWOOD irin su Tout too, The Ghost, The Millions and Diamonds in the Sky, da dai sauransu.

Jarumin yana da aure mata daya da yara biyu Ahmad da fatima

Alh Abdoul Embesey ii

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ali Nuhu Muhammad a Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma daga Balanga gari Jihar Gombe da mahaifiyarsa, da Fatima Karderam Digema daga Bama gidan gwamnatin jihar Borno. Ya girma a Jos da Kano.[1]

Aure[gyara sashe | gyara masomin]

ali nuhu yanada mata daya da Yara guda biyu Ahmad Ali nuhu da Fatima Ali nuhu.

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Ali ya yi karatu a Jami'ar Jos, Bayan karatun sakandare, ya sami digiri na farko a fannin ilimin na fasaha daga Jami'ar Jos. Yayi bautar kasa a Ibadan da ke jihar Oyo. Daga baya ya halarci Jami'ar Kudancin Kalifoniya don yayi kwas a fagen shirya fina-finai da fasahar sinima.[2]

Sana'ar fim[gyara sashe | gyara masomin]

Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne a shekarar ta 1999 mai suna “Abin sirri ne”. An fi saninsa da rawar da yake takawa a "Sangaya" wanda ya zama dayan finafinan Hausa da suka fi samun kudi a lokacin. Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama, wadanda suka hada da Azal, Jarumin Maza, da Stinda a matsayin fitaccen Jarumi a wajen bayar da gudummuwa a yayin bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy a (2007). A shekarar ta 2019, Ali Nuhu ya yi bikin cikarsa shekaru 20 a masana'antar nishadantarwa. Ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500).[3]


Mabiya[gyara sashe | gyara masomin]

inda akayi ittifaki akan yana da mabiya a Twitter sama da 140,000 da kuma mabiya a Facebook sama da 3,000,000 da kuma wasu a shafin Instagram sama da milyan 1,000,000.[4][5]

Fina finai a Kannywood[gyara sashe | gyara masomin]

(BT) na nufin Ba Tabbas, ma'ana babu tabbacin kwanan wata da shekarar da fim din ya fita. Yayin da akwai wasu kuma da ake da tabbacin kwanan watan fitar su.

Fim ↑ Shekara Fim Shekara
Abaya BT Alhini BT
Abin Sirri Ne 1998 Ali BT
Alhini BT Alkebba BT
Ali BT
Alkebba BT
Ambato BT
Aska Tara BT
Zuwa Da Kai BT
Uwar Miji BT
'Ya 'Ya Na BT
Ina Miji Na? BT
Gambiza BT
Namijin Duniya BT
Dama da Hauni BT
Ga Fili Ga Mai Doki BT
Masu Aji BT
Zo Mu Zauna BT
Mashi 2003
Gida da Waje BT
Yanayi BT
Farin Wata BT
Sakayya 1998
Harafin So BT
Zuciya Ko Ruhi BT
Sangaya 2000
JIGAL 2002
Bashin Gaba BT
Mai Gadon Zinare BT
Ragowar Yaki BT
Kishin Mata BT
Jurwaye BT
Fitilar Dare BT
Rana da Wata BT
Umarnin Uwa BT
Gadan Ga BT
Sabon Shafi BT
Hawan Girma BT
Khalid BT
Maraichi BT
Har Abada BT
Qiyasi BT
Shamsiyya BT
Tawakkali BT
Raliya BT
Maryam Diyana BT
Rawani BT
Ban Ga Masoyi Ba BT
Gidan Iko BT
Zamba BT
Kamilalla BT
Nazari BT
Garinmu da Zafi (Dawo-Dawo) BT
Bilal BT
Mujadala BT
Bahaushiya BT
Rariya 2017
Dangin Miji 2017
Ba Tabbas 2017
Mansoor 2017
Zuciya Da Hawaye 2017
Wacece Sarauniya? 2017
Jarumta 2016
Mu'amalat 2016
Dattijo 2016
Shinaz 2016
Igiyar Zato 2016
Halacci 2015
'Yar Tasha 2015
Wutar Gaba 2015
Bani Bake 2015
Gamu Nan Dai 2015
Uba da 'Da 2015
Baya da Kura 2015
Ba'asi 2015
Sallamar So 2015
Kurman Allo 2015
Nasibi 2015
Hanyar Kano 2014
Sirrin Da Ke Raina 2014
Mai Dalilin Aure (Match Maker) 2014
Jinin Jiki Na 2014
Garbati 2014
'Ya daga Allah 2014
Idan Hakane 2014
Kanin Miji 2014
Mati da Lado 2014
Sai a Lahira 2014
Munafikin Mata 2014
Duniyar Nan 2014
So Aljannar Duniya 2014
Hujja 2014
Hakkin Miji 2014
Andamali 2013
Dakin Amarya 2013
Nadawo Gareki 2013
Wani Gari 2013
Da Kishiyar Gida 2013
Haske 2013
Lamiraj 2013
Jarumin Maza 2013
Fari Da Baki 2013
Zuri'a 2013
Mai Jego 2013
Mai Farin Jini 2013
Halisa 2013
Matar Jami'a 2013
Kudi A Duhu 2013
Madubin Dubawa 2012
Gani Gaka 2012
Wani Hanin 2012
Kudi A Duhu 2012
Son Zuciya 2012
Dan Marayan Zaki 2012
Kara da Kiyashi 2012
Rai Dai 2012
Hubbi 2012
Bazan Barki Ba 2012
Son Mai So 2012
Blood and Henna 2012
Maza Da Mata 2012
Noor (The Light) 2012
Talatu 2012
Kona Gari 2012
Adamsy 2011
Alhaki Kwikwiyo 2011
Armala 2011
Malika 2011
Tsaraba 2011
Mutallab 2011
Mai Zamani 2011
Jaraba 2011
Ke Duniya 2011
Toron Giwa 2011
Fisabilillahi 2011
Muradi 2011
Rai Da Buri 2011
Ankwa 2011
'Yan Mata 2010
Mai Ladabi 2010
Sarauta 2010
Kukan Zaki (the Lion’s Cry) 2010
Balaraba 2010
Ladidin Baba 2010
Dan Sarki 2010
Sai Wata Rana 2010
Wasila 2010
Artabu (A Mazauna) 2009
Dijangala 2008
Hafsah 2007
Bana Bakwai 2007
Sabon Sarki 2006
Jamhuriya 2005
Taurari 2005
Gwamnati 2003
zero hour 2020

Bada umarni[gyara sashe | gyara masomin]

Shekara Suna Matsayi Salo Kamfanin daya shirya
2007 Sitanda Jarumi Wasa
2011 Carbin Kwai Jarumi Wasa
2012 Madubin Dubawa Jarumi Wasa
2012 Last Flight to Abuja Jarumi Wasa Nollywood Film Factory
2013 Blood and Henna Jarumi Wasa Newage Networks
2013 Confusion Na Wa Jarumi Was Cinema KpataKpata
2013 Wani Hanin Jarumi Wasa
2014 Matan Gida Jarumi Wasa
2015 Jinin Jikina Jarumi Wasa
2016 Nasibi Jarumi Wasa
2016 Ojukokoro Jarumi Wasa Singularity Media
2017 Banana Island Ghost Jarumi Wasa

Lamban girma[gyara sashe | gyara masomin]

Ali Nuhu yana daga cikin jaruman fina-finan Hausa wadanda ke gaba-gaba wajen samun gagarumar nasarori a masana'antar ta Kannywood dama ta mutanen kudancin Najeriya wato Nollywood. Anan zamu kawo maku wasu daga cikin kyaututtukan da Ali Nuhu ya samu a harkar sa ta shirya fina-finai.[6][7]

Shekara Kyauta Rukuni Sakamako
2005 Arewa Films Award Best Actor
2007 3rd Africa Movie Academy Awards Best Upcoming Actor award Nasara
2008 The Future Award Best Actor Nasara
2011 Zulu African Film Academy Awards Best Actor (Indigenous)
2012 2012 Best of Nollywood Awards Best Actor (Hausa) Nasara
2013 9th Africa Movie Academy Awards Best Supporting Actor Nasara
2013 2013 Nigeria Entertainment Awards Best Actor Nasara
2013 2013 Best of Nollywood Awards Best Actor (Hausa) Nasara
2013 City People Entertainment Awards Kannywood Face Nasara
2014 Kannywood Awards Best Actor Nasara
2014 Leadership Awards Best Artiste Nasara
2014 City People Entertainment Awards Best Actor Nasara
2014 City People Entertainment Awards Kannywood Face Nasara
2014 Arewa Music and Movie Awards Pride of Kannywood Nasara
2014 Arewa Music and Movie Awards Best Actor (Popular) Nasara
2015 19th African Film Awards Most Outstanding Actor Nasara
2015 2015 Best of Nollywood Award Best Actor (Hausa) Nasara
2015 2015 Kannywood Awards Best Actor (Popular) Nasara
2015 City People Entertainment Awards Kannywood Personality Nasara
2016 2016 Best of Nollywood Awards Best Actor (Hausa) Nasara
2016 Arewa Music and Movie Awards Best Actor Nasara
2016 Kannywood Awards Best Actor Nasara
2016 City People Entertainment Awards Kannywood Face Nasara
2016 Arewa Creative Industry Awards Entertainment Award Nasara
2016 Wazobia FM’s COWA Awards Excellent Entertainer Nasara
2017 Northern Nigeria Peace Awards Best Actor Nasara
2017 City People Entertainment Awards Kannywood Face Nasara
2017 City People Entertainment Awards Best Actor Nasara
2017 2017 Best of Nollywood Awards Special Recognition Award An dakatar

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]

Ali Nuhu

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Yanzu Jama'a Sun Fara Fahimta Da Rungumar Ayyukanmu-In Ji Jarumi Ali Nuhu". voahausa.com. Voice of America. Retrieved 13 October 2017.
  2. https://www.voahausa.com/a/a-39-2005-08-06-voa1-91733284/1370189.html
  3. Lere, Mohammed (15 January 2019). "Ali Nuhu celebrates 20 years in Kannywood". Premium Times. Retrieved 25 November 2019.
  4. https://www.premiumtimesng.com/entertainment/kannywood/305949-ali-nuhu-celebrates-20-years-in-kannywood.html
  5. https://www.legit.ng/1216404-ali-nuhus-biography-family-career.html
  6. "Sharia Affected Cinema Culture In Northern Nigeria – Nuhu". leadership.ng. Leadership Newspaper. Archived from the original on 13 October 2017. Retrieved 13 October 2017.
  7. "Ali Nuhu honoured with Doctorate by Cotonou University – Daily Trust". Daily Trust (in Turanci). 2018-10-10. Archived from the original on 2018-10-10. Retrieved 2018-10-11.