Aminu Waziri Tambuwal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aminu Waziri Tambuwal
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

13 ga Yuni, 2023 -
District: Sokoto South
gwamnan jihar Sokoto

Mayu 2015 - 29 Mayu 2023
Aliyu Magatakarda Wamakko
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 29 Mayu 2015 - Abdussamad Dasuki
District: Tambuwal
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
Dimeji Bankole - Yakubu Dogara
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
Rayuwa
Cikakken suna Aminu Waziri Tambuwal
Haihuwa Tambuwal, 10 ga Janairu, 1966 (58 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Usmanu Danfodiyo
Matakin karatu Bachelor of Laws (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Lauya
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Aminu Waziri Tambuwal (An haife shi a ranar 10 ga watan Janairu, a shekara ta alif ɗari tara da sittin da shida 1966) miladiyya, a garin Tambuwal da ke yankin kudancin jihar Sakkwato, wanda kuma ya fito daga zuri’ar Wazirin masarautar Tambuwal.

Bayan somawa ko farawa da neman ilimin addini, sai ya soma neman ilimin zamani daga makarantar firamare ta Tambuwal, daga nan kuma sai ya zarce zuwa kwalejin horas da malamai ta gwamnati da ke Dogon-Daji inda ya kammala da samun takardar shaidar malanta mai daraja ta II a shekara ta alif 1984. Daga nan sai ya samu gurbin karatun gaba da sakandare a jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto, inda ya kammala da samun digirin farko a bangaren shari’a a shekarar alif 1991, haka kuma a bisa tanadin dokokin karatun shari’a, ya halarci makarantar horas da lauyoyi da ke Legas inda bayan karɓar horo na shekara daya, sai aka tabbatar da shi a matsayin cikakken lauya a shekarar alif 1992.

Ko bancin karance-karance lamurran da suka shafi shari’a, Honarabul Tambuwal ya kuma halarci kwasa-kwasai iri-iri a ƙasashen ƙetare wadanda suka haɗa da na sanin ƙa’idojin sha’anin sadarwa wato ‘Telecoms Regulatory Master Class-Bath’ a Ƙasar Ingila a shekarar 2004, sai kuma kwas akan shata dokokin da suka jibanci bangaren sadarwa, wato ‘Lawmaking for the Communications Sectors’ a BMIT da ke Johannesburg ta ƙasar Afirka ta Kudu a shekarar 2004, har wa yau, ya halarci wani kwas akan yadda za a sanya ido akan tafiyar da kamfani a cikin tsari irin na gwagwarmayar neman kasuwa, wato ‘Regulating a Competitive Industry’ a Brussels ta kasar Beljiyam a shekarar 2005, a jami’ar Tulane kuwa, ya halarci kwas na tsara dokokin majalisa na kasa da kasa wato ‘International Legislative Drafting’ a shekara ta 2005, ya halarci wani kwas akan cusa ra’ayi da daidaita matsaya wato ‘Influence and Negotiation’ a shahararriyar makarantar kasuwanci ta Stanford wato, ‘Stanford Graduate makarantar kasuwanci’ a shekarar 2008, da wasu kwasa-kwasai da dama.

Aminu Tambuwal Da Sarkin Musulmin Yayin Ziyara Da Aka Kawo Musu a Sokoto

A karon farko, an kuma zaɓi honarabul Aminu Waziri Tambuwal a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kebbe da Tambuwal a majalisar wakilai ta kasa a shekarar 2003, a karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta ANPP. Tun daga wannan lokacin tauraruwar farin jinin siyasarsa ta ci gaba da haskawa inda ya taba rike shugaban marasa rinjaye, ya kuma taba rike mukamin mataimakin babban mai tsawatarwa a zauren majalisar, mukamin da ya ci gaba da rikewa har zuwa karshen tafiyar majalisar wakilai zubi na shidda. Kuma ya taba zama jagoran ayarin ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya a nahiyar Afirka da Karebiyan da kuma gamin gambizar tawagar ‘yan majalisun kungiyar kasashen tarayyar Turai. Haka ma ya taba zama wakilin yanki na kungiyar ‘yan majalisun dokoki na kungiyar kasashe renon Ingila.

Honarabul Aminu Waziri, memba ne a majalisar zartaswa ta kungiyar lauyoyi ta kasa wato NBA, haka ma memba ne a kungiyar lauyoyi ta duniya, haka memba ne a kungiyar tsofaffin daliban makarantar koyon sha’anin gwamnati ta tsohon shugaban Amurka John F Kennedy, wato Kennedy School of Government’ da ke jami’ar Harvard ta kasar Amurka. Memba ne a kungiyar tsofaffin daliban makarantar koyon sha’anin kasuwanci ta Stanford wato Stanford Graduate School of Business’ da ke Amurka, memba ne a kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Tulane ta Amurka. 

A gida Nijeriya, honarabul Tambuwal ya sami lambobin yabo da na karramawa iri-iri, kamar digirin girmamawa a fannin shari’a da jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato ta ba shi, domin yabawa da kwazonsa da kuma kokarinsa na ciyar da kasa gaba.

Aminu Waziri Tambuwal yayi takarar gwamnan jihar Sokoto a shekara ta 2015 karkashin jam'iyyar adawa ta APC, kuma yayi nasarar lashe zaben wanda ya bashi damar zama Gwamnan jihar ta Sokoto. Wanda daga bisani ya koma jam'iyyar sa ta farko wato PDP. Wanda itace jam'iyyar adawa a yanzu.

A yanzu haka Aminu Waziri Tambuwal shine mataimakin Shugaban Gwamnonin Najeriya, Wanda Gwamna Kayode Fayemi ke Jagoranta.

Kuma shugaban Gwamnonin Babbar Jam'iyyar Hamayya ta PDP.

Kuma yanzu haka yana cikin mutanen da ake ganin zasu iya maye gurbin Shugaba Buhari, inda ake fatan Jam'iyyar sa ta PDP ta bashi tikitin tsayawa takara a babban zaɓen shekara ta 2023 In Sha Allah. Daga sirajo design

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]