Bauchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bauchi
Wikimedia disambiguation page (en) Fassara

Bauchi ƙasa ce dake yankin Arewacin Nigeria tana yankin Arewacin gabashin Nigeria an kirkiri jihar Bauchi ne a watan Fabrairun shekarar 1976 daga tsohuwar jihar Arewa maso Gabas ta gwamnatin Janar Murtala Mohammed. Asali ta hadane da yankin Gombe, wadda ta zama jiha ta daban a shekarar 1996. Tana da kananan hukumomi Ashirin 20. Babban birninta shi ne Bauchi. Jihar Bauchi tana yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, tana da fadin murabba'in kilomita 45,837. Jihar Bauchi tana iyaka da Kano da Jigawa daga arewa sai Yobe da Gombe daga gabas sai jihar Kaduna ta yamma da Filato da Taraba a kudu. Gaba daya yankunan yammacin jihar da arewacin kasar suna da tsaunuka da duwatsu. Hakan ya faru ne sakamakon kusancin jihar da tsaunukan Jos ta jihar Plateau da kasar Cameroun. Jihar Bauchi na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da suka mamaye yankunan ciyayi guda biyu, wato Sudan Savannah da Sahel Savannah. Manyan koguna guda biyu ne suka ratsa jihar, kogin Gongola da Hadejia. Yanayin yanayin jihar Bauchi yana da zafi sosai a watannin Afrilu da Mayu, yayin da Disamba da Janairu ne watanni mafi sanyi. Jihar Bauchi na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da suka mamaye yankunan ciyayi guda biyu, wato Sudan Savannah da Sahel Savannah. Manyan koguna guda biyu ne suka ratsa jihar, kogin Gongola da Hadejia. Yanayin yanayin jihar Bauchi yana da zafi sosai a watannin Afrilu da Mayu, yayin da Disamba da Janairu ne watanni mafi sanyi. Jihar Bauchi tana da ƙabilu masu yawa, wanda sun kai ƙabilu 55 da suka haɗa da Fulani, Gerawa, Sayawa, Jarawa, Kirfawa, Turawa Bolewa, Karekare, Kanuri, Fa'awa, Butawa, Warjawa, Zulawa, Boyawa MBadawa. Amma Fulani su ne ƙabila mafi Yewa a Jahar,inda suka mamaye kananun hukumomi irinsu Toro, jama'are, giade, darazo, katagum, misau, Alkaleri, dambam, da dai sauran su. Wannan yana nufin cewa suna da asali,da tsarin sana'a, da sauran abubuwa da yawa waɗanda ke cikin kasancewar al'ummar jihar.

ASALIN SUNA[gyara sashe | gyara masomin]

An samo Sunan garin Bauchi ne daga sunan wani Baushe wanda ya kasance jajirtaccen mafarauci a zamaninsa. Baushe shine ya fara zama a Bauchi kafin zuwan Malam Yakubu Sarkin Bauchi na farko. Bauchi a cewar masu fassarar Hausa na farko na nufin “babu wata dabba da ta tsira daga tarko da kibiryar Baushe”. Akwai kamanceceniyar al'adu a tsakanin kabilun jihar, ayyukan sana'a, bukukuwa, sutura da kuma yawan mu'amalar ƙabilanci musamman wajen zaman aure da tattalin arziki. Wasu daga cikin ƙabilun suna da alaƙar barkwanci da ke tsakanin su, misali; Fulani da Kanuri, Jarawa da Sayawa, da sauransu.

TATTALIN ARZIKI[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Bauchi jihar noma ce. Sunada Faɗin ƙasa mai albarka hakan yasa yana ƙara fa'ida ga kayan amfanin gonar da suke samarwa, waɗanda suka haɗa da masara, shinkafa, gero, gyada. Ana yin noma da tallafawa ta hanyar amfani da madatsun ruwa kamar dam na Balanga da sauransu. Haka nan ana kiwon shanu da sauran dabbobi a jihar. Haka kuma jihar tana da masana’antun da suke samar da kayayyakin Amfanin Al'umma na yau da kullum.

YAWAN BUDE IDO[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Bauchi na da albarkar wuraren yawon bude ido da dama. Jihar Bauchi tana da wurin ajiyar Dabbobi na Yankari (mafi girman kiwo a Afirka ta Yamma), Premier Game Reserve, Rock Paintings a Goji da Shira, Gidan Tarihi na jiha Shehu Azare Park Tunga Dutse Wikki Warm Springs Yankari National Park (Game Reserve).

BUKUKUWAN AL'ADA[gyara sashe | gyara masomin]

Amanya Festival Bikin Fasaha da Al'adu na Jahar Bauchi Idin kaciya na mutanen Gezawa Durbar Festival Kokowa and Dambe Festival Lake Efi Fishing Festival Bikin Al'adun Yankari

Bikin Daba (Durbar) babban abin jan hankali ne na shekara-shekara[1]

KANANAN HUKOMOMI[gyara sashe | gyara masomin]

Birnin Bauchi na cikin ƙananan hukumomi ashirin da ke jihar Bauchi:

Bauchi, Tafawa Balewa, Dass, Toro, Bogoro, Ningi, Warji, Ganjuwa, Kirfi, Alkaleri, Darazo, Misau, Giade, Shira, Jamaare, Katagum, Itas/Gadau, Zaki, Gamawa da Dambam.[2]


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "A 100-Year-Old Muslim Festival of Horse Riding"
  2. "Bauchi State List of Local Governments Zip codes | Nigeria Zip Codes"