Hukumar Labarai ta Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Hukumar Labarai ta Najeriya
Bayanai
Gajeren suna NAN
Iri news agency (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Abuja
Tarihi
Ƙirƙira 1976
nannewsngr.com

Da turanci News Agency of Nigeria (NAN), Hukumace mai tace labarai da rahotanni na kasa baki ɗaya wanda gwamnatin tarayyar Nijeriya ke gudanar da ita kaman dai tashan telebijin na NTA.[1] An kuma kafa NAN ne daga cikin wasu dalilai don yada labarai a yankunan daban daban na kasa da kuma yankunan wajen Najeriya kuma don ta zama hanya na daƙile labarai na ƙarya game da Najeriya.[2]

An kafa hukumar ne a 10 ga watan Mayun shekarata 1976, kuma an fara gudanar da aiki a 2 Oktoba 1978 .[3] A Manajan Daraktan na Agency ne Dame Oluremi Oyo.(OON).

NAN na gabatar da labaranta ga masu kallo a kanun labarai guda uku a duk rana. Sashin yanar gizo na hukumar itace www.nannews.ng (a baya can www.nan.ng) wanda aka gabatar a ranar 8 ga watan Agustan shekarar 2016 don watsa labarai a duk fadin duniya musamman ga masu ra'ayin sauraren labarai game da Najeriya, kasar da tafi kowacce kasa yawan jama'a a Afirka.

Hukumar na da dumbin manema labarai da dama a sassa daban daban na kasar suna samo labarai masu mahimmanci daga tushen gaskiya wanda gidajen jaridu na kasa da na yankuna ke wallafawa musamman wadanda basu iya samun labarai a ko ina a fadin kasa.[4] Akwai kudade da ake biya kafin a samu irin wadannan labarai.[5]

Shekarun ritaya daga NAN[gyara sashe | gyara masomin]

Mista Bayo Onanuga, Darekta mai kula da harkokin NAN, ya buƙaci ƙarin yawan shekarun ajiye aiki ga ma'aikatan NAN daga shekaru 60 zuwa shekaru 70. Bayo yayi wannan kira ne a yayin bikin ajiye aiki na Mataimakin babban jami'i a hukumar. Dangane da ra'ayinsa, ma'aikatan jarida na samun ƙwarewa na musamman a lokacin da suka tsufa, inda ya buƙaci ƙungiyoyi da ke da alhaki da su daukaka al'amari zuwa hukumomin da suka dace. Ya kamata a kara yawan shekarun ajiye aiki ga 'yan jarida don basu daman bada gudummawa ga ma'aikatunsu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ahmed, Amir. "Saudi Arabia turns back 1,000 female pilgrims from Nigeria." CNN. Friday 28 September 2012. Retrieved on 29 September 2012.
  2. Babatunde Abdulfatai & May 2004, p. 22.
  3. "Who Are We? Archived 2012-10-08 at the Wayback Machine" News Agency of Nigeria. Retrieved on 29 September 2012.
  4. Babatunde, Abdulfatai. "ASSESSING THE USE OF THE SERVICES OF THE NEWS AGENCY OF NIGERIA (NAN) BY NIGERIAN NEWSPAPERS".
  5. "Subscription to News Agency of Nigeria (NAN)"

Mahaɗa[gyara sashe | gyara masomin]