Abbas Njidda Tafida

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sake dubawa tun a 20:28, 4 Nuwamba, 2021 daga Mr. Sufie (hira | gudummuwa) (Sabon shafi: Mai martaba Alhaji Abbas shine sarki na goma sha biyu (12) a daular masarautar Muri, kuma ya hau sarautar ne a shekarar 1988 biyowa bayan cire sarki Alhaki Umaru Abba Tukur daga karagar mulki. HAIHUWA An haifi mai martaba sarkin Muri Alhaji Abbas Njidda Tafida a ranar 10 ga watan shida na shekarar 1953 a cikin garin Jalingo babban fadar jihar Taraba. Alhaji Abbas ya kasance daga tsatson marigayi Lamido Nya Jatau wanda ya kafa garin Jalingo kuma jika ne ga Lamido Mafindi, sarki...)
(bamban) ←Canji na baya | Zubi na yanzu (bamban) | Canji na gaba → (bamban)

Mai martaba Alhaji Abbas shine sarki na goma sha biyu (12) a daular masarautar Muri, kuma ya hau sarautar ne a shekarar 1988 biyowa bayan cire sarki Alhaki Umaru Abba Tukur daga karagar mulki. HAIHUWA An haifi mai martaba sarkin Muri Alhaji Abbas Njidda Tafida a ranar 10 ga watan shida na shekarar 1953 a cikin garin Jalingo babban fadar jihar Taraba. Alhaji Abbas ya kasance daga tsatson marigayi Lamido Nya Jatau wanda ya kafa garin Jalingo kuma jika ne ga Lamido Mafindi, sarki na tara a daular. KARATU Mai martaba Alhaji Abbas bayan karatun Islamiya da na alkurani da yayi, ya shiga makarantar firamari na Mohammadu Nya Primary School dake garin Jalingo a shekarar 1961 har lokacin kammalawa a shekarar 1967. Bayan kammala makarantar firamarin, mai martaba ya ci gaba da karatunshi na sakandari a Government College Keffi wanda yake a jihar Nasarawa a yau a shekarar 1967 zuwa shekarar 1973. Bayan kammala makarantar sakandari, mai martaba ya sami takardan shiga Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1973 inda yayi karatun digirin shi a fannin kasuwanci kuma ya kammala a shekarar 1977. Mai martaba ya kuma yi karatun PGD a fannin tattalin arzikin a African Development Bank, Abidjan a shekarar 1981 zuwa 1982. Har ila yau, ya kuma kara yin wani karatun na PGD a makarantar Green Beheld Smith and Co., London a shekarar 1982 zuwa shekarar 1983. Ayyuka Mai martaba ya kasance gwarzon dan kasuwa kuma shararren manomi. A shekarar 1978 zuwa shekarar 1979 ya yi aiki da hukumar New Nigeria Development Company (NNDC). Mai martaba ya kasance babban manaja (MD) na Nigeria Hotels daga shekarar 1979 har ya zuwa shekarar 1988 lokacin da aka nada shi sabon sarkin Muri. An dai nada mai martaba sabon sarki ne a ranar 12 ga watan Yulin shekarar 1988 don maye gurbin marigayi tsohon sarki Alhaji Umaru Abba Tukur. Mai martaba Alhaji Abbas dai ya kasance sarki na goma sha biyu a daular Muri. . <https://www.voahausa.com/a/5548728.html\> . <https://m.youtube.com/watch?v=zkKXFTI_\>

<https://commons.m.wikimedia.org/wiki/File:Emir_Of_Muri_Alh_Abbas_Tafida.jpg\>

<https://dailyrealityng.com/2021/07/30/emir-of-muris-eid-speech-and-matters-therein/>