Yusuf Abdullahi Falgore

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sake dubawa tun a 07:11, 7 Nuwamba, 2021 daga Mr. Sufie (hira | gudummuwa) (Sabon shafi: An haifi Yusuf Abdullahi a garin Falgore dake karamar hukumar Rogo ta jihar Kano (1953). A tsakanin 1963 – 1969 ya halarci Falgore Central da Gwarzo Senior Primary School. Daga nan ya wuce Kwalejin Malamai ta Bichi a shekarar 1970 kuma ya kammala a shekarar 1974. Daga 1975 – 1978 ya halarci Makarantar Advance Teachers College, Zariya, ya kuma fito da takardar shaidar karatu ta kasa (NCE). Daga nan ya wuce babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (1981 – 1983) don yin di...)
(bamban) ←Canji na baya | Zubi na yanzu (bamban) | Canji na gaba → (bamban)

An haifi Yusuf Abdullahi a garin Falgore dake karamar hukumar Rogo ta jihar Kano (1953). A tsakanin 1963 – 1969 ya halarci Falgore Central da Gwarzo Senior Primary School. Daga nan ya wuce Kwalejin Malamai ta Bichi a shekarar 1970 kuma ya kammala a shekarar 1974. Daga 1975 – 1978 ya halarci Makarantar Advance Teachers College, Zariya, ya kuma fito da takardar shaidar karatu ta kasa (NCE). Daga nan ya wuce babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (1981 – 1983) don yin digiri a fannin Ilimi. An zabi Honorabul Falgore Shugaban Karamar Hukuma ba Jam’iyya, sannan ya zama Shugaban riko (Sau biyu) 1991 – 1993, 2002 – 2003 bi da bi. An kuma zabe shi a Majalisar Dokoki ta Jiha sau biyu, 2011 – 2015 sai 2015 – 2019 bi da bi, kuma ya rike kakakin majalisar jahar kano na yan watanni kafin a tsigeshi a.maye guebinsa da Gambo a shekarar 2011. Kafin ya shiga siyasa Honorabul Falgore ma’aikaci ne a ma’aikatar ilimi ta jiha. Hon. Falgore tsohon kakakin shi ne Shugaban Kwamitin Gudanarwa da Nasiha tsakanin 2011 - 2015 ya jagoranci Kwamitin Majalisar kan Ilimin Sakandare.

</https://www.premiumtimesng.com/tag/yusuf-abdullahi-falgore/>

</https://allafrica.com/stories/>

</https://www.bbc.com/hausa/news/2011/12/111220_tsigekaki/>