Muhammad Uba Gurjiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sake dubawa tun a 22:18, 7 Nuwamba, 2021 daga Mr. Sufie (hira | gudummuwa) (Sabon shafi: An haifi Muhammad Uba Gurjiya a shekarar 1982 a garin Gurjiya dake karamar hukumar Bunkure. Ya yi karatun firamare a makarantar Gurjiya Central Primary School, Bunkure Junior Secondary School 1994-1996 da Senior Secondary School a Famous School for Arabic Studies (SAS) Kano tsakanin 1997-2000 bi da bi. A tsakanin 2000-2003 ya halarci Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano inda ya yi kwas dinsa na NCE da Jami'ar Bayero ta Kano (2006-2010) inda ya yi digirinsa na ilimi. Ya rike kwamitoci...)
(bamban) ←Canji na baya | Zubi na yanzu (bamban) | Canji na gaba → (bamban)

An haifi Muhammad Uba Gurjiya a shekarar 1982 a garin Gurjiya dake karamar hukumar Bunkure. Ya yi karatun firamare a makarantar Gurjiya Central Primary School, Bunkure Junior Secondary School 1994-1996 da Senior Secondary School a Famous School for Arabic Studies (SAS) Kano tsakanin 1997-2000 bi da bi. A tsakanin 2000-2003 ya halarci Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano inda ya yi kwas dinsa na NCE da Jami'ar Bayero ta Kano (2006-2010) inda ya yi digirinsa na ilimi. Ya rike kwamitoci da dama ciki har da na Kudi Ya shiga aikin hukumar kula da ilimi ta kasa (SUBEB) kuma ya kasance jami'in cibiya ta karamar hukumar Bunkure tsawon shekaru 4. ya taba zama malamin ajujuwa kafin a zabe shi a shekarar 2015 don wakiltar'karamar Hukumar Bunkure a Majalisar Jiha. ya kuma lashe zaben sa a shekarar 2019.

</ http://avarinlogspot.blogspot.com/2020/02/kano-assembly-removes-majority-leader.html?m=1/>

</https://www.today.ng/topic/muhammad-uba-gurjiya\>