User talk:Abuihisan

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
                                                    HUDUBARMU TA YAU


                                                     HADARI ZALUNCI

                                             DAGA MIMBARIN ABU HURAIRA (RA), SOKOTO

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Ya al’ummar musulmi! Addinin musulunci addinin Allah ne da ya shinfida hanyoyin zaman lafiya da jin dadin rayuwa. Daga cikin manya manyan dokokin ubangiji shi ne ya wajabta adalci kuma ya haramta cuta. Wadannan dokokin Allah ya dora su har ga kansa. Don haka, Allah Tabaraka Wa Ta’ala ba ya zalunci kuma ba ya bari a zalunci bayinsa. Allah Ta’ala yana cewa: {إِنَّ اللَّهَ لاَ يَظْلِمُ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ} [النساء:40]. {وَمَا اللَّهُ يُرِيدُ ظُلْماً لّلْعَالَمِينَ} [آل عمران:108]. A hadisul kudsi ga abinda Allah ke cewa: ((يا عبادي، إني حرمت الظلم على نفسي، وجعلته بينكم محرماً، فلا تظالموا)) الحديث. A cikin dukkan addinan da Allah ya saukar ba in da bai haramta zalunci ba, Gashi ko dan adam an halicce shi da son yin zalunci da cuta kamar yadda Allah ya ce: {إِنَّ الإنْسَانَ لَظَلُومٌ كَفَّارٌ} [إبراهيم:34]. {إِنَّا عَرَضْنَا الأمَانَةَ عَلَى السَّمَاواتِ وَالأرْضِ وَالْجِبَالِ فَأبَيْنَ أَن يَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الإِنْسَانُ إِنَّهُ كَانَ ظَلُوماً جَهُولاً} [الأحزاب:72]. Al-Hafiz Ibnu Kayyim al-Jauziyyah yana cewa: Duk asalin kowane alheri abu biyu ne: Ilmi da adalci. Haka kuma duk asalin kowane sharri daga jahilci ne da zalunci. Idan Allah yana son alheri ga mutum sai ya sanar da shi abinda ke amfaninsa, sai ya kawar da jahilci, sannan ya ba shi ikon amfani da shi sai ya gusar da zalunci. Duba Igathatul Lahfan (2/136-137). Hadarin zalunci ya sa manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya shelanta haramcinsa a taro mafi girma kuma mafi daraja da musulmi suka taba yi a zamaninsa. Hadarin zalunci yana kara hauhawa idan ya kasance ya auka ma jama’a masu yawa, ko wadanda aka sani ko wadanda ba a sani ba. Wannan shi ya sa manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya tsananta maganar cin dukiyar ganima kafin a raba ta kuma ya ce, { عار ونار وشنار على أهله يوم القيامة } kuma da aka kashe wani yaronsa da ake ce ma Mid’am sahabbai suka ce, muna yi masa murnar shiga aljanna, sai manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, sam. Na rantse da Allah yana can yana ci da wuta a kan bargon da ya dauka daga cikin ganimar Khaibar. Da jin haka sai wani sahabi ya yi sauri ya dawo da saitin takalma guda daya da ya dauka. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, ka kuru, domin da sun zame ma ka takalma biyu na wuta. Kafin mu fadi irin hadurran da ke tattare da zalunci bari mu diba irin tsawatawar da Allah Ta’ala ya yi dangane da shi: { وَالظَّالِمِينَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا}. وقال تعالى: {وَمَن يَظْلِم مِّنكُمْ نُذِقْهُ عَذَابًا كَبِيرًا}. {وَتَرَاهُمْ يُعْرَضُونَ عَلَيْهَا خَاشِعِينَ مِنَ الذُّلِّ يَنظُرُونَ مِن طَرْفٍ خَفِيٍّ وَقَالَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ الْخَاسِرِينَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَأَهْلِيهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَلَا إِنَّ الظَّالِمِينَ فِي عَذَابٍ مُّقِيمٍ}. {إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمْ سُرَادِقُهَا وَإِن يَسْتَغِيثُوا يُغَاثُوا بِمَاء كَالْمُهْلِ يَشْوِي الْوُجُوهَ بِئْسَ الشَّرَابُ وَسَاءتْ مُرْتَفَقًا}. Kuma shi zalunci ba ya da kadan. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce: Duk wanda ya ci zalun wani mutum da karfi Allah zai haramta ma sa aljanna ya wajbta ma sa wuta. Sai wani ya ce, ya manzon Allah, ko da abin kadan ne? sai Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, “Ko da karen aswaki ne”. Muslim ya ruwaito shi. Daga cikin manyan bala’oin da zalunci ke haifarwa akwai: 1. Hana zaman lafiya da ci gaba الَّذِينَ آمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ أُولَئِكَ لَهُمُ الْأَمْنُ وَهُمْ مُهْتَدُونَ 2. Gamuwa da hukuncin Allah. Hadisi ya bayyana cewa, Allah Ta’ala azabta wata macce a kan kyanwa. To, in aga bawan allah mummuni, ina kuma ga al’umma mai dinbin yawa wadanda kila ba ka san iyakar su ba!! 3. Allah ba ya son azzalumai: وَتِلْكَ الْأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيْنَ النَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَيَتَّخِذَ مِنْكُمْ شُهَدَاءَ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ 4. Kuma ya debe ma azzalumai albarka أَلَا لَعْنَةُ اللَّهِ عَلَى الظَّالِمِينَ 5. Zalunci yana haifar da duhu ga mai yin sa ranar alkiyama, ranar da kowa ke bukatar haske don tsallake siradi. Kamar yadda hadisi ya zo cewa: ((الظُّلم ظلماتٌ يوم القيامة)) (أخرجه البخاري (5/100 الفتح) ومسلم (2579) عن ابن عمر). 6. Zalunci yana janyo halaka ga al’umma {وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ مِن قَبْلِكُمْ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَاءتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيّنَاتِ} [يونس:13]. (( فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ أَبْوَابَ كُلِّ شَيْءٍ حَتَّى إِذَا فَرِحُواْ بِمَا أُوتُواْ أَخَذْنَاهُم بَغْتَةً فَإِذَا هُم مُّبْلِسُونَ * فَقُطِعَ دَابِرُ الْقَوْمِ الَّذِينَ ظَلَمُواْ وَالْحَمْدُ لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ )) (44-45:الانعام). ((وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ مِن قَبْلِكُمْ لَمَّا ظَلَمُواْ)) (13:يونس). (( وَتِلْكَ الْقُرَى أَهْلَكْنَاهُمْ لَمَّا ظَلَمُوا وَجَعَلْنَا لِمَهْلِكِهِم مَّوْعِداً )) (51: الكهف). 7. A kullum wanda ke zalunci ba ya rabuwa da Allah ya isa. Wannan ko yana da matukar hadari. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce ma Mu’az bin Jabal Radiyallahu Anhu: «Ka kiyayi «Allah ya isar» wanda aka zalunta, don ba ta da shamaki tsakanin ta da Allah». Haka kuma sayyidina Abu Huraira Radiyallahu Anhu ya ruwaito daga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama cewa: «Addu’ar mutum ukku Allah na karbar su: «Wanda aka zalunta da Matafiyi da Mahaifi». Kana can kana sharar bacci, kana ta sakin hansari, hankalinka a kwance, ba ka tunanin kome, shi kuma wannan bawan Allah yana can yana dako, sai dare ya kai tsakiya ko ya kusa karewa, a cikin duhu zai tashi, cikin natsuwa ya yi alwala ya kabbarta sallah.. idan ya kai goshinsa ga kasa sai ya tartsa ma Allah kuka, a daidai lokacin da Allah ke shelar: «Ina mai kirana in karba ma sa?» «Ina mai neman agajina in agaza ma sa?». Ana haka ne zai kai karar ka ga buwayayyen sarki. Don haka ne sai ka ga kwatsam! al’amarin mutum ya dagule, basirarsa ta toshe, dabararsa ta kare, jarinsa ya kare, ikonsa ya gushe, lafiya ta karanta, jin dadi ya kau, jama’a sun watse, an bar shi da tarin zunubi, da yawan bakin ciki da karancin jin dadi ..Wannan duk karamin aikin Allah ya isa kenan. Wannan shi ne abin da sarki Khalid al-Barmaki ya fada ma dansa lokacin da aka tsare su a kurkuku, yaron ya ce, Baba! dubi halin da muka fito kuma dubi yanayin da muka samu kanmu. Sai sarki Khalid ya ce ma sa, Allah dai ya kiyaye. Watakila wani ne ya yi mana “Allah ya isa» muna can muna bacci. Wani fursuna ya yi ma sarki Khalid bin Abdillah al-Kasari wa’azi mai kama da haka a lokacin yana gwamnan Khurasan sai ya kai ziyara gidan kaso yana raba ma fursunoni kyauta. Da ya kawo ga wannan bawan Allah sai ya ce ma sa: In don ka tausaya kake bayarwa to, tausaya ma kanka daga wanda ka zalunta. Yi hattara da wanda bai da kowa sai Allah, bai da wani makami sai addu’a. Ka sani kofofin sama gaba daya budewa su ke in an ce, “Allah ya isa». Ga nasihar da wani mawaki ya yi: لا تظلمنَّ إذا ما كنت مقتدراً فالظلم ترجع عقباهُ إلى الندم تنامُ عيناك والمظلوم منتبه يدعو عليك وعينُ الله لم تنم Wani kuma sai ya ce: أما والله إن الظلم شؤم وما زال المسيء هو الظلوم ستعلم يا ظلوم إذا التقينا غداً عند المليك من الملوم 8. Azzalumi ba ya taba samun rabauta. Saurari abinda annabin Allah Yusuf Alaihis Salam ya ce a lokacin da matar maigidansa ta neme shi da ya ci amanarsa: ((وَرَاوَدَتْهُ الَّتِي هُوَ فِي بَيْتِهَا عَنْ نَفْسِهِ وَغَلَّقَتِ الْأَبْوَابَ وَقَالَتْ هَيْتَ لَكَ قَالَ مَعَاذَ اللَّهِ إِنَّهُ رَبِّي أَحْسَنَ مَثْوَايَ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ)) 9. Allah ba ya shiryar da azzalumi ((أَجَعَلْتُمْ سِقَايَةَ الْحَاجِّ وَعِمَارَةَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ كَمَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَجَاهَدَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ لَا يَسْتَوُونَ عِنْدَ اللَّهِ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ)) 10. Azzalumi zai gamu da gamonsa tun a nan duniya ((فَذَرْهُمْ حَتَّى يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي فِيهِ يُصْعَقُونَ يَوْمَ لَا يُغْنِي عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنْصَرُونَ * وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا عَذَابًا دُونَ ذَلِكَ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ)) 11. A ranar alkiyama azzalumi yana da ban tausai: ((وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ)) (227: الشعراء) . {وَلاَ تَحْسَبَنَّ اللَّهَ غَافِلاً عَمَّا يَعْمَلُ الظَّالِمُونَ إِنَّمَا يُؤَخّرُهُمْ لِيَوْمٍ تَشْخَصُ فِيهِ الأبْصَارُ * مُهْطِعِينَ مُقْنِعِى رُءوسِهِمْ لاَ يَرْتَدُّ إِلَيْهِمْ طَرْفُهُمْ وَأَفْئِدَتُهُمْ هَوَاء} [إبراهيم:42، 43]. {مَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ حَمِيمٍ وَلاَ شَفِيعٍ يُطَاعُ} [غافر:18] {وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ} [البقرة:270] A rannan ne azzalumi zai nemi ba da fansa da duk abinda ya mallaka, ciki har da dan jarinsa na duniya, kai da ma duk abinda ake so in zai samu. Amma ina! (( وَلَوْ أَنَّ لِكُلِّ نَفْسٍ ظَلَمَتْ مَا فِي الأَرْضِ لاَفْتَدَتْ)) (54:يونس) (( وَلَوْ أَنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا مَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعاً وَمِثْلَهُ مَعَهُ لَافْتَدَوْا بِهِ مِن سُوءِ الْعَذَابِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَبَدَا لَهُم مِّنَ اللَّهِ مَا لَمْ يَكُونُوا يَحْتَسِبُونَ)) (47:الزمر) . 12. Ba yadda za a yi a shiga aljanna tare da digon zalunci domin kuwa ko bayan tsallaka siradi ba a shiga aljanna har sai an kawar da zalunci kowane iri, an kwatar ma kowane mai alhaki hakkinsa. Abu Sa’id al-Khudri Radiyallahu Anhu ya karbo daga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama cewa, “Idan mummunai suka tsallaka siradi za a tsayar da su a kan wata gada da ke tsakanin aljanna da wuta sai a caje su da wasu laifukka na zalunci da suka gudana a tsakanin su. Sai an gama tsarkake su tsabal sannan ayi ma su iznin shiga aljanna”. Sannan manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya yi rantsuwa cewa, idan suka shiga aljanna kowa zai gane gidansa fiye da yadda ya ke gane gidansa na duniya. Sahihul Bukhari (2440). Allah Ta’ala ya yi gaskiya: وَالَّذِينَ قُتِلُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَلَنْ يُضِلَّ أَعْمَالَهُمْ * سَيَهْدِيهِمْ وَيُصْلِحُ بَالَهُمْ * وَيُدْخِلُهُمُ الْجَنَّةَ عَرَّفَهَا لَهُمْ Ya ku bayin Allah! Da yawa mukan yi kuskure in mun ji ana ruwan ayoyi game da zalunci da azzalumai sai mu ce, sarakuna sun halaka! Kaicon masu mulki! Bone ya tabbata ga alkalai!!! Babu in da ba a iya samun zalunci a cikin zamantakewa ta rayuwa. Akwai zalunci a ciniki, akwai shi a bashi, akwai a kwadago, akwai a auratayya, akwai a makwautaka, akwai malanta. Haka kuma akwai shi a magana, akwai a kallo, akwai har a batun zucci ta hanyar miyagun zace-zace. Idan ka sa mutum aiki ka rage ma sa hakkensa kai azzalumi ne. idan ka yi algussu a cikin sana’arka kai azzalumi ne. Idan ka sare icce wanda mutane suke shan inwa kai azzalumi ne. Idan aka yi yarjejeniya da kai ka saba kai azzalumi ne. Idan ka kwance sharadi kai azzalumi ne. Idan macce ta debi kayan gidan mijinta ba da izninsa ba ita azzaluma ce. Idan miji ya kasa ba matarsa hakken kwanciya ko na abinci ko karantarwa ko kulawa da lafiyarta shi azzalumi ne. Kai, idan ma ya kasa ba ta alhakinta na zaunawa su yi fira, da jiyar da ita dadin rayuwar macce da namiji shi azzalumi ne. Haka kuma azzalumi ne idan ya kasa daidaita alhakin matansa ko ‘ya’yansa. Babu shakka shugaba in ya zamo azzalumi to, hadarinsa ya fi girma wannan shi ya sa za a zo da kowane shugaba koda na mutum goma ne a daure ranar alkiyama sai dai in ya yi adalci adalcin nasa ya warware shi kamar yadda ya tabbata a cikin hadisi. Duba Sahihul Jami’ 5571 da Silsila Sahiha 344. Zalunci mataki ukku ne: 1. Mafi hadarinsu shi ne wanda ya danganci hakkin Allah kamar Shirka. Sai kuma sauran zunubbai da Allah ya hana. 2. Zaluntar bayin Allah. Mafi hadari daga cikin zaluntar bayin Allah shi ne zubar da jininsu, sannan cin mutuncinsu, sannan kwace ko satar dukiyarsu. 3. Mutum ya zalunci kansa ta hanyar aikata abinda zai halaka shi ko ya sa shi cikin kunci a nan duniya ko a gobe kiyama. Idan an zalunce ka ya zaka yi? akwai matakai guda uku, wanda duk kayi babu laifi a kanka: 1. Ka rama daidai yadda aka zalunce ka in kana da iko {وَلَمَنِ انتَصَرَ بَعْدَ ظُلْمِهِ فَأُوْلَئِكَ مَا عَلَيْهِمْ مّن سَبِيلٍ} [الشورى:41]. 2. Ka roki Allah ya rama maka, ko ya kwatar ma ka hakkinka {لاَّ يُحِبُّ اللَّهُ الْجَهْرَ بِالسُّوء مِنَ الْقَوْلِ إِلاَّ مَن ظُلِمَ وَكَانَ اللَّهُ سَمِيعاً عَلِيماً} [النساء:148]. 3. Ka yafe saboda Allah خُذِ الْعَفْوَ وَأْمُرْ بِالْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ الْجَاهِلِينَ * وَإِمَّا يَنْزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ إِنَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ Wadannan matakan gaba daya Allah Ta’ala ya fade inda yake cewa: {وَالَّذِينَ إِذَا أَصَابَهُمُ الْبَغْىُ هُمْ يَنتَصِرُونَ * وَجَزَاء سَيّئَةٍ سَيّئَةٌ مّثْلُهَا فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ إِنَّهُ لاَ يُحِبُّ الظَّالِمِينَ * وَلَمَنِ انْتَصَرَ بَعْدَ ظُلْمِهِ فَأُولَئِكَ مَا عَلَيْهِمْ مِنْ سَبِيلٍ} [الشورى:39-41]. Ya ku bayin Allah! wanda ya fada a cikin zalunci alhakinsa a kan mu shi ne mu taimake shi. Ya zamu taimake shi? wannan shi ne abinda sahabbai suka tambayi manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama a lokacin da ya ce, “Ka taimaki dan uwanka ko shi ke zalunci ko shi aka zalunta”. Amsar da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ba su ita ce, taimakon azzalumi shi ne a kange shi a hana ma sa yin zalunci. Allah Ta’ala na iya yi wa azzalumi talala amma ba zai taba kyale shi ba. Sau da yawa kuma Allah ya ke sallade wani azzalumi don ya darkake wani. Kamar yadda madaukakin sarki ya ce: (( وَكَذَلِكَ نُوَلِّي بَعْضَ الظَّالِمِينَ بَعْضاً بِمَا كَانُواْ يَكْسِبُونَ)) (129:الانعام) Don haka ne wani malami ya ce: وما من يد إلا يدُ اللهِ فوقَها ولا ظالمٍ إلا سُيبلى بظالم A nan duniya azzalumi na iya samun girma da kima ko don kwadayin abin hannunsa ko don gudun sharrinsa, amma a ranar alkiyama babu wulakantacce marar daraja da kima irin sa. Sai dai yana da kyau mu sani cewa, kome girman zalunci yana da tuba kamar yadda madaukakin sarki ya ce: {وَمَن يَعْمَلْ سُوءاً أَوْ يَظْلِمْ نَفْسَهُ ثُمَّ يَسْتَغْفِرِ اللَّهَ يَجِدِ اللَّهَ غَفُوراً رَّحِيماً} [النساء:110]. ((إِلَّا مَن ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسْناً بَعْدَ سُوءٍ فَإِنِّي غَفُورٌ رَّحِيمٌ )) (11: النمل). (( فَمَن تَابَ مِن بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ)) (المائدة:39). Don haka, Allah ya bude kofa gare ka ya kai dan adam mai yawan zalunci. Ka tuna duk irin nau’in jama’ar da ka zalunta. Sannan ka bi hanyar sasantawa da su tun ba a tafi lahira ba suka nemi ladarka sa’adda ka fi kome bukatuwa zuwa gare ta, kuma a rannan kana ji kana gani za a ba su ladar azuminka da umrarka da sauran ibadarka. An gabatar da ita a ranar 2 ga jimada Akhir 1432H

AMFANIN BANKIN MUSULUNCI


FASSARAR HUDUBA DAGA MASALLACIN SHEIK JA'AFAR MAHMUD ADAM, TUDN MURTALA KANO,

30/7/1432=1/7/2011.

Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, shi ne mafi sanin abin da kowanne dan Adam ke boyewa a zuciyarsa da abinda yake bayyanawa ina gode masa ina jinjina masa. Dukkan salati ya tabbata ga manzon Allah s.a.w shugaban dukkan halitttu gaba daya, wanda shine mai ceton kowa da kowa. Bayan haka yaku jama’a kuji tsoran Allah ku tsoraci dalilan saba masa da azabarsa ku bar abin da Allah yace ku bari matukar dai ku muminai ne. ku bar cin riba don tana daga cikin abin da yake jawo fushin Allah , tana daga cikin manyan laifuka masu halakarwa. Allah (s.wt) yace ‘Yaku wadanda sukay I imani kuji tsoran Allah kuma ku bar abin day a saura na daga riba matukar dai ku muminai ne idan ba zaku bari ba ku shirya yaki da Allah da Manzonsa . Bakara. Allah yace” wadanda suke cin riba baza su tashi basai kamar wanda shedan ya shafe shi saboda suna cewa shi cikin ai kamar riba ne. to allah ya halatta ciniki amma ya haramta riba, wanda duk wa’aziyazo masa masa ya kuma bari, toabin day a wuce komai a kansa lamarinsa nag a Allah. Amma wanda ya komawa riba to wadannan sune ‘yan wuta zasu dauwama a cikinta. Allah ya shafe albarka riba ya rubanya albarkar sadaka. Allah baya son dukkan wani kafiri mai sabo bakara. Assheikh Abdurrahman sa’adu yace; yace Allah ya ambaci Azzulumai maciya riba masu mummunar mu’amala za’ saka musu da irin abin da suka yin a cin riba anan duniyaa wajen neman abincinsu, ranar alkiyma kuma idan zasu tashi daga kabari irin yadda wanda aljani ya shafa yake tashi ta haka zasu rika tashi suna faduwa.Allah ya shiryar damu amin. Hadisi ya tabbata a muslim. Hadisin jabir yace; “Annabi s.w.a ya tsinewa duk mai cin riba da wanda ya bayar da wanda ya rubuta da mai bada sheda, yace duk daidai suke MENENE RIBA KUMA MENE NE BAMBANCIN TSAKANIN RIBA DA RIIBA ? Sheikh Ragim astihani yana cewa riba itace dan abinda ake samu idan an syar da kaya ma’aan dimiyar da ake kasuwanci don ita. Da riba da riiba duk kari ne a kasuwanci don haka ne ma mushrikai suke cewa duk dayana amma akwai bambamci a tsakani musamman ma rihbar fifiko. BAMBAMCI TSAKANIN RIBA DA RIIBA. Yadda zamu bambambace kuwa dole ne mu saka kowanne a ama’uni da shari’a ta dora shi don mu gane abubuwan da suke kawo riba guda uku ne. 1. Idan ka bawa wani kudi ya juya, idan an samu riiba ku raba an samu riiba ku raba, shi ake kra mudaraba. 2. Mutum yayi kasuwanci da kansa dukiyarsa yaci riiiba. 3. Mutum ya karbi dukiyar wani ya juya su raba riibar,. Idan muka duba da kyau za muga cewa akwai bambamci mai fadi tsakanin riba da riiba, don haka ita riba ba a mata wahala, kana kake dorawa mai bashi ko ciniki ka fifita wani akan wani kayan da irinsu daya yayin ciniki. Kamar cinikin dawa da dawa ko fifita wani akan wata. To riba ta shiga. BAMBAMCI TSAKANIN RIBA DA KUDIN KWADAGO Ibnu munzur yana cewa. Kudin kwadago shi ne abin da aka baka don kayi wata wahala wato dai ladan aikin da kayi bayan ka gama aka biya ka, kamar magini ko kafinta ko manomi da dai sauransu. Haka kudin hayar gida ko dako ko ofis duk yana shiga wannan idan muka duba da kyau za muga cewa akwai bambanci sosai tsakanin riba da kudin kwadago wato ladan wahalar kwadago ya halatta amma, ita riba bata halatta ba kamar yadda ya gabata. Don haka cinikin da mutum yayi aka biya shi babu wanda kya canacnta wannan hakki sai dai wanda ya aikata kamar ma’aikacin gwamnati da yayi aiki bias gaskiya da rikon amana da kula da lokaci da bin dukkan ka’idojin da aka saka to kaga ya cancanci albashinsa don kwadago yayi. Haka kudin da aka baiwa lauya don kare ka shari’a matukar yayi gaskiya a aikinsa shima dan kawadago nehalak yaci ba riba ba. SAMAR DA BANKUNAN MUSULUNCI Rayuwar mu a yau ta kullu da harkokin banki, hart a kai babu wani mai hankali mawadaci da ba zai iya harka da da banki ba, musamman ma a fagen kasuwanci da sana’o I bankunan da muke tare da su a ayu sun jawo wa jama’a da dama arziki da asara to ina mafita? Mafita itace dole ne a samara da bankunan da zasu kula da duk abin day a zama dole akan su su kuma toshe duk wata kafa ta barna, wadannan bankuna sune na musulunci. Lallai ne a samara da bankunan musulunci don su tsarkakewa ala’ummar mu dukiyar su daga kazantar riba a cikin wannan kasa tamu Najeria. Dole musulmi su maid a hankali su kan wannan harka, kuma don amfaninsa. Hakan kuwa zai yiwu domin duk bin da ake so akwai shi a hannun musulmi. Kudin tsarin mulkin kasa bai haramta ba. Saboda haka akwai kalubale a gabans sosai. Abin da ke kara tabbatar da hakan shine wasu kasashe na musulmai datuni suka yi haka. Wato sun bude bankunan musulunci. In har wasu zasu yi to wasu ma zasu iya babu abin da zai hana masulmai a Najeria yayi yunkuri akan banakin musulunci . matukar dai dalilan smar dahis sun cika to dalilin cin nasarar kuwa sun cika. In har bankunan da bana na musulunci ba zasu rike kansu ta kowacce irin hanya to ya kamata na Musulunci suma su bi irin hanyoyin shari’a kamar yaddad suke a rubuce. Hanyoyin da dama wadanda shari’a ta tsara don cin riba na kai tsayar da kuma wadanda ban a kai tsaye bane, kamar su mudaraba da makarada da muja’ara da makamntansu. Allah ya sakawa gwamnan babban bankin Najeria da alkhari shi kadai ne ya fito yake ta babatun tabbatar da wannan tsari na samar da bankin musulunci a kasan nan a yanzu. Malamai da shugabannnis da ‘yan siyasa dake majalisa sun ja bakunansu sun yi shiru mun kasa tabuka komai ko da na karfafa gwiwa ga wannan bawan Allah. Ya daukake shi ya taimake shi ya kuma kare shi . MISALAN WASU BANKUNAN MUSULUNCI. Bankin Musulunci ba sabon Abu bane, domin kasashe da daama ne suka farar aiwatar dashi shekaru masu yawa kamar bankin Nasir Alijtima’I na kasar Misra, wanda aka kafa shi a shekara 1972, bayan an cika ka’idojinsa a shekara 1971 ya fara aikin da jari imanin miliyan goma sha hudu 14,000,00 na Junaihar misri ya shiga fagen tattalin arziki a duniya a shekara ta 1973. RIIBAR DA WANNAN BANKI YACI Bayan y agama biyan nauyin da yake kansa ya sami kashi 6% a shekara ta 1973 sannan ta kaishi kashi 9.5% a shekara ta 1975 da 1979 ta karu a shekara ta 1980 har ta kaishi 10% haka nan ya samu kashi 125%a shekarar 1981 a shekera ta 1982 ribar su ta karye ta dawo kashi 11.4% Idan ka kula a shekara ta 1982 an samu tawaya a cikin riibar da ak samu da ma kuma haka harkar kasuwanci take a Musulunci, akwai riiba da faduwa a akasuwanci. Awani bangaren kuma bankin yana da ma’aikata mai zaman kanta ta kula da zakka wannan ma’aikata it ace take tara zakka ga dukkan mao son ya bayar da nasa kason, ta hanyar kananan kungiyoyi wadanda suke tara a masallatai da cikin Unguwanni kananansu da manyansu. Yawan wadannan Kungiyoyi yana karuwa domin tun suna 120 a shekara ta 1973 har suka kai 700 a shekara ta 1979 kamar yadda abin da ake samu ya karu daga Junaiha dubu ashirin da a shekara ta 1973 ya zuwa 531,000 dubu dari biyar da talatin da daya, a shekara ta 1977, yawan masu bada zakka a wannan banki sun kai kimanin dubu ashirimn da uku, (23) a shekara ta 1977 Bankin said a ya rabawa kimanin mutane dubu arba’ain da shida 46,0000 daga wanann abin day a samu. Kamar yadda ya ciyar a wuirare daban-daban kamar makaranta na haddar kur’ani yara da malamansu gwiwa haka kuma sun tashi tsaye wajen gina masallatai da makarantu manya da kanana. Sun maida hankalinsu wajen gina asibitoci da wuraren koyar da sana’o I wannanya fito a fili karara wajen bayyana irin riibar da fa’idojin da bankin Musulunci ke iya samu idan an kafa shi don gashi wannan cikin ‘yan shekara kadan da kafa shi har ya cimma nasarori da dama ta fuskar bunkasa tattalin arzikin Musulunci wannan kasa misra. Don haka bankunan musulunci sun zama wajibi a kafa su don ta hanyar sun e kadai za a iya rage ko magance talaucin day a gallabi jama’ar kasar nan. Allah ka daukaka Musulunci da musulmai, ka kaskantar da kafirci da kafirai, ka yiwa rayuwarmu albarka, ka zaunar da kasarmu lafiya. Allah ka gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu a dalilin ambaliyar rowan sama day a shafi mutanen Fagge, da Dakata da sauran wurare. Allah ya mayarwa da wadanda suka rasa dukiyayinsu da mafi alkharin abins da suka rasa. Wasallalahu ala nabiyinia Muhammad(s.a.w).


DAGA DR. IMAM ABDULLAHI SALEH PAKISTAN Phd.