Rukuni:Kira

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

sana'ar ƙira tana daga cikin manyan daɗaɗɗun kuma muhimman sana'o'in kasar Hausa . Sana'ar kira sana'a ce wadda take da ɗimbin tarihi a ƙasar hausa kuma kusan maƙera sune suke ƙera mafi yawan kayan aikin sana'o'in hannu irin su noma, kwanuka da sauransu.Sana’ar Ƙira sana’a ce da ake sarrafa ta da ƙarafa, zinari ko azurfa, da dama ko sauran dangogin ƙarfe a mayar da su abin amfani na yau da kullum don sauka ka rayuwa.

NAU'O'IN ƘIRA AKASAR HAUSA[gyara sashe | gyara masomin]

Idan muka lura acikin ta'arifin damukayi zamu ga ita Ƙira ta kasu kashi biyu, akwai ƙirar fari da kuma ƙirar baƙi. Ga bayanin su ɗaya bayan ɗaya.

Ƙirar fari shine ƙera kaya da ake Amfani da su wajen ado/kawa. Wanda waɗannan kaya zaka samu mata su sukafi amfani dasu misali.

  1. sarƙa
  2. Dan kunne
  1. Awarwaro
  1. Masilla
  1. Barima ds.ds

Ƙirar baki shine ƙirar kayan aiki musamman wanda ake amfani dasu wajen noma ko yaƙi irin su.

  1. Takobi
  1. Adda
  1. Mashi
  1. Kibya/kifiya
  1. Fatanya
  1. Garma
  1. Manjagara ds.ds
KAYAN AIKIN ƘIRA A ƘASAR HAUSA[gyara sashe | gyara masomin]

Maƙera inda ake aikin sarrafa ƙarfe.

Uw'ar maƙera karfenda ake dora ƙarfe domin sarrafa sa.

Gawayi makamashi hura wuta.

Guduma shine dunkulallan ƙarfe mai ƙota wanda ake dukan ƙarfe dashi.

Kasko ana saka ruwa ne a cikin sa domin sanyaya karfe bayan an dukeshi.

Gizago ana amfani dashi wurin sassaka ɓota.

Matsoni shine ake amfani dashi wurin hada karfe.

zugazugi fatar tunkiya ko akuya ake dinkawa ayi mata baki da ƙarfe domin hura wuta'

Madashi Da shi ake huda ƙota bayan an saka shi a wuta ya yi ja.

Masaba]] ƙarfe ne da ake amfani dashi wurin dukan ƙarfe.

Kurfi shine ake amfani dashi wurin sara ƙarfe.

Awartaki shine ake amfani dashi wurin ciro ƙarfe awuta domin sarrafa sa.

A halin yanzu babu shafuka a wannan category.