Ɗanwake

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ɗanwake
Kayan haɗi Wake, borkono, Man gyaɗa, Tumatir, Gurji, Kwai, Bao Bao (en) Fassara da albasa
Tarihi
Asali Najeriya
Farawa 1960
danwake DA kayan ganye
Danwake da kwai

ƊanwakeƊanwake, abinci ne da galibi al'ummar Hausawa ne sukafi yin shi, Ɗanwake ya kasance abincin mar-mari ne domin ba kasafai akanyi shi ba. Ana Kuma yin shi da fulawa,alkama ko garin danwake da kuma dawa. Idan an gama shi ana cin shi da man gyada da yaji. Wasu na sa mai kabeji da albasa da kwai.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Ɗanwake ya samo asali ne tun lokacin da manoma suka fara shuka amfanin gona, inda ake amfani da wani daga cikin irin nau'in abincin da ake Nomawa wajen sarrafa shi ya zama Ɗanwake.

Kayan Ɗanwake[gyara sashe | gyara masomin]

Kayan da ake amfani da su wajen hada Ɗanwake sun haɗa da Dawa,Rogo,Kanwa,Barkono,kuka,Mai ko Manja,Ruwa mai ƙyau da dai sauran su.

Yadda ake ɗanwake[gyara sashe | gyara masomin]

Da farko dai za'a wanke dawa, a shanyata ta bushe, sai a haɗa da rogo akai niƙa. Bayan an niƙa sai a tankade shi da rariya sai a saka kuka a ƙwafa shi da ruwan kanwa sannan a rinka jefa shi a cikin tafasasshen ruwan zafi da ke a kan wuta, bayan yayi tafasa ukku a lokaci ya hadu za'a kwashe sai a soya mai ko Manja domin a sanya cikin ɗanwaken, sai a dauki yaji a barbaɗa ko mage sai ci kawai. [1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-12-02. Retrieved 2021-03-15.