Internationaler Bund (wanda aka fi sani da: IB ) (Turanci: International Federation) ƙungiya ce ta ilimi ta Jamus wadda ba ta da alaƙa da siyasa kuma ba ta da alaƙa da ƙungiyoyin addini . An kafa IB a shekarar 1949 [1] kuma tana ɗaya daga cikin manyan masu ba da sabis a fannoni na shirye-shiryen zamantakewa da ilimi don ci gaban matasa a Turai tare da ƙungiyar sa kai mai rijista (Jamusanci: Eingetragener Verein ), ƙungiyoyin sa kai masu zaman kansu, kamfanonin kasuwanci, shirye-shiryen ilimi da makarantu da kwalejojin fasaha. [2] [3] [4] [5] [6] A yau, IB tana da wurare kusan 700 a wurare sama da 300 a faɗin Jamus kuma tana haɓaka ayyukan ilimi da yawa a ƙasashen waje tare da cibiyoyin ilimi a China, Georgia da Turkiyya da kuma tare da Stiftung Internationaler Bund Polska a Poland, [7] [8] da sauransu. [9] IB tana da hedikwatarta a Frankfurt, Jamus. [10] [11]