Ƙungiyar Ƴan Tawaye Moro

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Group half.svgƘungiyar Ƴan Tawaye Moro
MNLF flag.svg
Bayanai
Iri jam'iyyar siyasa

mnlfnet.com


Facebook icon 192.png
Tutar MNLF

Kungiyar ‘yan tawayen Moro ta MNLF kungiya ce ta ƴan tawaye a ƙasar Philippines . [1] Nur Misuari ne ya fara kafa ta a shekarar 1969. Ƙungiyar MNLF tana gwagwarmaya da gwamnatin Philippines don neman ‘ yancin yankin Bangsamoro . A cikin shekarun da suka gabata an yi ƙoƙari da yawa don cimma zaman lafiya tsakanin MNLF da gwamnati. A cikin 1976 kungiyar Hadin gwiwar Musulunci ta shirya yarjejeniya amma hakan ya faskara. A shekarar 1986 Shugaba Corazon Aquino ya sadu da Misuari, kuma a shekarar 1989 aka baiwa yankin matakin cin gashin kai. Shugaba Fidel Ramos ya shirya yarjejeniyar zaman lafiya a 1996 wanda ya ba da damar a zaɓi Misuari a matsayin gwamnan yankin. Misuari ya jagoranci wani tawaye na adawa da gwamnatin tarayya a 2001, amma hakan ya faskara kuma aka tura shi kurkuku. MNLF ya ce yankin Bangsamoro Land ya game Sulu, Mindanao, Palawan da Sabah (a Malaysia ). MNLF memba ne Ƙungiyar Hadin Kan Islama .

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Encyclopædia Britannica Online, s. v. "Moro National Liberation Front (MNLF)", accessed 20 February 2016, http://www.britannica.com/topic/Moro-National-Liberation-Front.

Sauran yanar gizo[gyara sashe | Gyara masomin]