Jump to content

Ƙungiyar Haɗin kai ta Tanzaniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ƙungiyar Haɗin kai ta Tanzaniya
Bayanai
Iri cooperative (en) Fassara
Ƙasa Tanzaniya
Tarihi
Ƙirƙira 1961

Ƙungiyar Haɗin kai ta Tanzaniya, wadda aka fi sani da suna Ƙungiyar Haɗin kai ta Tanganyika,[1] ƙungiya ce ta ƙasa ta ƙungiyoyin haɗin gwiwa a ƙasar Tanzaniya.[2] Ƙungiyar ta yi rajista a shekarar 1994 da wasu membobi daga ƙasar Tanzaniya, da suka haɗa da; Auduga, Coffee, Tobacco, Cashew, Cereal da ma sauran ƙungiyoyin masana'antun Noma.

Gwamnatin Tanzaniya ce ta fara kafa ko assasa ƙungiyar a matsayin Ƙungiyar Haɗin kai ta Tanganyika a shekara ta 1961,[3] tare da zummar manufar ƙarfafa haɓakar ci-gaban haɗin gwiwa na ire-iren waɗannan ƙungiyoyi. Fadada yunƙurin haɗin gwiwa wani ɓangare ne na shirin ƙara bunƙasa tattalin arziki na gwamnati na shekaru biyar a tsakanin shekarar 1964 ya zuwa 1969.

  1. Nkebukwa, Anna (1989). Proceedings of the seminars in women's involvement in co-operatives in Tanzania held in Dar-es-Salaam. University of Dar-es-Salaam.
  2. "Welcome to Tanzania Federation of Cooperatives LTD". Ushirika. Archived from the original on 25 March 2013. Retrieved 6 April 2013.
  3. Lyimo, Francis Fanuel (2012). Rural Cooperation: In the Cooperative Movement in Tanzania. African Books Collective. ISBN 998708155X.