Ƙwayoyin Cutar Sikila
Appearance
| Ƙwayoyin Cutar Sikila | |
|---|---|
![]() | |
| Description (en) | |
| Iri |
autosomal recessive disease (en) blood protein disease (en) |
| Field of study (en) |
hematology (en) |
| Genetic association (en) |
NPRL3 (en) |
| Therapy (en) | |
| Magani |
sodium phenylbutyrate (en) |
| Identifier (en) | |
| ICD-10-CM | D57, D57.1, D57.2, D57.20, D57.3, D57.8 da D57.0 |
| ICD-9-CM | 282.6, 282.60 da 282.63 |
| OMIM | 603903 |
| DiseasesDB | 12069 |
| MedlinePlus | 000527 |
| eMedicine | 000527 |
| MeSH | D000755 |
| Disease Ontology ID | DOID:10923 |
Ƙwayoyin Cutar Sikila SCD-(Sickle cell disease), wanda kuma ake kira sickle cell, rukuni ne na cututtukan jini masu alaƙa da haemoglobin da aka gada.[1] Mafi yawan nau'in da aka fi sani da sickle cell anemia[2] Yana haifar da rashin daidaituwa a cikin haemoglobin mai ɗauke da iskar oxygen da ake samu a cikin jajayen ƙwayoyin jini.[3] Wannan yana haifar da ƙwayoyin jajayen jini suna ɗaukar siffa mara kyau kamar sikila a wasu yanayi; da wannan siffa, ba sa iya gurɓatawa yayin da suke wucewa ta capillaries, suna haifar da toshewa.[4]
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Cutar amosalin jini tana faruwa ne idan mutum ya gaji kwayoyin halitta guda biyu marasa kyau na kwayar β-globin da ke samar da haemoglobin, daya daga mahaifiya daya kuma daga mahaifi. Kwayar halittar da ba ta dace ba tana samar da haemoglobin S (HbS) wadda ke canza yanayin kwayoyin jajayen ƙwayoyin jini. Rikicin sikila yana faruwa ne a lokacin da kwayoyin jajayen ƙwayoyin jini suka canza daga siffar da ta saba kamar kwano zuwa siffar kamar lauje ko jaririn wata , wanda hakan ke iya toshe ƙananan hanyoyin jini; cutan na iya tashi wa mutum sakamakon canjin yanayin zafi, damuwa, rashin ruwa a jiki, da kuma tsayin wuri kaman kan dutse. Mutumin da ke da kwayar halitta mara kyau guda ɗaya ba ya yawan samun alamun cutar kuma ana cewa yana da dabi'ar sikila, waɗannan mutane kuma ana kiransu masu ɗaukar kwayar cutar. Ana gano cutar ta hanyar gwajin jini. Wasu ƙasashe suna gwada dukan jarirai da suka haihu don cutar.[l Ana kuma iya gano cutar a cikin ɗan tayin da ke cikin ciki kafin a haife sa.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "What Is Sickle Cell Disease?". National Heart, Lung, and Blood Institute. 30 September 2024. Re
- ↑ "What Is Sickle Cell Disease?". National Heart, Lung, and Blood Institute. 30 September 2024. Retrieved
- ↑ What Is Sickle Cell Disease?". National Heart, Lung, and Blood Institute. 30 September 2024. Retrieved 26 October 2024
- ↑ What Is Sickle Cell Disease?". National Heart, Lung, and Blood Institute. 30 September 2024. Retrieved 26 October 2024.
- ↑ https://www.nhlbi.nih.gov/health/sickle-cell-disease/causes
