Zaɓen gwamnan jihar Gongola, 1979
| Iri |
gubernatorial election (en) |
|---|---|
| Kwanan watan | 28 ga Yuli, 1979 |
| Ƙasa | Najeriya |
| Applies to jurisdiction (en) | Jihar Gongola |
An gudanar da zaben gwamnan jihar Gongola a shekarar 1979 a ranar 28 ga Yulin 1979.[1] Abubakar Barde na GNPP ya lashe zabe a karo na farko inda ya zama gwamna na farko a jihar Gongola da kashi 47.6% inda ya doke dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta NPN Ahmed Mahmudu Ribadu[1][2] wanda ya samu kashi 34.6 cikin 100 a fafatawar.
Abubakar Barde ya zama dan takarar GNPP bayan ya doke abokin takararsa na kusa, Wilberforce Juta, wanda daga baya ya zama mataimakinsa, a zaben fidda gwani na jam’iyyar da tazarar kuri’u uku kacal.[3][4]
Tsarin zabe
[gyara sashe | gyara masomin]An zabi Gwamnan Jihar Gongola ne ta hanyar amfani da tsarin kada kuri’a.
Sakamako
[gyara sashe | gyara masomin]Uku daga cikin jam’iyyun siyasa biyar da hukumar zabe ta tarayya (FEDECO) ta yi wa rijista ne suka shiga zaben. Abubakar Barde na jam'iyyar GNPP ne ya lashe zaben da kuri'u mafi girma na kashi 47.6%. Adadin wadanda suka yi rajista sun kai 2,284,500. An kada kuri'u 650,725.[5][6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Muhammad, Zayyad I. "Adamawa Governorship 2007; A Fuzzy Rumble, Steep Marathon!". Gamji. Retrieved 28 May 2021
- ↑ Analysis: Nuhu Ribadu And Adamawa 's Urgent Need For Paradigm Shift". News Diary Online.com. Retrieved 28 May 2021.
- ↑ Ochetenwu, Jim (15 August 2020). "Adamawa declares 3-day mourning as former Gov Wilberforce Juta dies". Daily Post. Retrieved 28 May 2021.
- ↑ A Former Governor, Juta Is Dead". News Lounge. 16 August 2020. Retrieved 28 May 2021
- ↑ Hart, C. (1993). "The Nigerian Elections of 1983" (JSTOR). Africa: Journal of the International African Institute. 63 (3): 397–418. doi:10.2307/1161428. JSTOR 1161428. S2CID 145591693.
- ↑ Reasons why the Tiv and Jukun are in war". The Nation Online. 29 July 2019. Retrieved 28 May 2021.