Aawatif Hayar
7 Oktoba 2021 - 23 Oktoba 2024 ← Jamila El Moussali | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Afourar (mul) | ||
| ƙasa | Maroko Faransa | ||
| Karatu | |||
| Makaranta | École normale supérieure - PSL (mul) (1989 - 1992) | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | telecommunications engineer (en) | ||
| Employers | Hassan II University of Casablanca EURECOM (en) | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | Istiqlal Party (en) | ||
Aawatif Hayar 'yar siyasa ce 'yar ƙasar Morocco kuma tsohuwar shugabar Jami'ar Hassan II ta Casablanca. Ta kasance Ministar Haɗin Kai, Haɗakar Jama'a da Iyali daga shekarun 2021 zuwa 2024 [1] [2]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Hayar tana da digiri na biyu a fannin Injiniyanci na Lantarki (1992) daga École normale supérieure Paris-Saclay da kuma digiri na uku a fannin Sarrafa Sigina da Sadarwa (2001) daga Cibiyar Fasaha ta Ƙasa ta Toulouse. [1] [3]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Daga shekarun 2001 zuwa 2010, Hayar ta yi aiki a matsayin mai bincike da koyarwa a EURECOM da ke Faransa. [1] [4]
A shekarar 2011, ta zama farfesa a Jami'ar Hassan II Casablanca. A shekarar 2016, an naɗa Hayar a matsayin mai ba da shawara kan kimiyya na Smart City Expo Casablanca da kuma shugabar babban taron IEEE International Smart Cities Conference. [4] [5]
Daga shekarar 2019 zuwa 2021, ta yi aiki a matsayin Shugabar Jami'ar Hassan II Casablanca. [5]
A watan Oktoban 2021, an zaɓi Hayar a matsayin Ministar Haɗin Kai, Haɗakar Jama'a da Iyali, [1] muƙamin da ta bari bayan shekaru 3. [6]
Kyaututtuka
[gyara sashe | gyara masomin]An naɗa Hayar a matsayin ɗaya daga cikin mata 10 mafi kirkire-kirkire a Afirka ta Gidauniyar Kirkire-kirkire ta Afirka a shekarar 2015. [1] [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 4 5 "Aawatif Hayar, Morocco's New Minister of Solidarity, Social Integration". Morocco World News (in Turanci). 8 October 2021. Retrieved 2023-06-16.
- ↑ "Experts of the Committee on the Elimination of Discrimination against Women Praise Morocco for Legislation Prohibiting Discrimination, Ask about High Maternal Mortality and Female Illiteracy Rates in Rural Areas". OHCHR (in Turanci). Retrieved 2022-10-07.
- ↑ "Aawatif Hayar". IEEE. Retrieved 2023-02-14.
- 1 2 3 "Qui est Aouatif Hayar ministre de la Solidarité, de l'Insertion sociale et de la Famille ?". www.challenge.ma (in Faransanci). 7 October 2021. Retrieved 2023-06-16.[permanent dead link]
- 1 2 "Aawatif Hayar". World Bank Live. Retrieved 2023-05-09.
- ↑ Kasraoui, Safaa (2024-10-23). "Who is Naima Ben Yahia, Morocco's New Minister of Solidarity". Morocco World News (in Turanci). Retrieved 2026-01-21.