Jump to content

Abba Isa Tijani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abba Isa Tijani
shugaba

- Olugbile Holloway (en) Fassara
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a museologist (en) Fassara

Abba Isa Tijani farfesa ne a Najeriya Farfesa a fannin ilmin tarihi da sanin halayyar dan adam. A shekarar 2020 aka nada shi babban darakta na hukumar kula da gidajen tarihi da tarihi ta Najeriya (NCMM).[1]

Daga 2005 zuwa 2008 Tijani ya yi aiki a Makarantar Gabas da Nazarin Afirka a Jami'ar London a kan wani aikin bincike da Cibiyar Nazarin Arts and Humanities Research Council ta dauki nauyinsa. Daga nan sai ya shiga Jami’ar Maiduguri, inda ya kasance Mataimakin Farfesa a fannin Ilimin Tarihi da Anthropology, Daraktan Riko na Cibiyar Nazarin da Ci Gaban Dorewar Al’adu, Shugaban Sashen Fine da kere-kere da kuma Mataimakin Darakta na Sashin Taswirar Jami’ar.[2]

An naɗa Tijani darakta janar na NCCM a watan Satumba 2020.[1] Ya taimaka wajen sasantawar dawo da tagulla na Benin daga jami'o'in Burtaniya guda biyu, Jami'ar Aberdeen da Kwalejin Jesus, Cambridge, a cikin Oktoba 2021.[3]

Sauran ayyukan

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Borrowing time: ethnoarchaeology at the Institute : exhibition catalogue. London: Museum Studies Department, Institute of Archaeology, University College, 1994.
  • (with Mala M. Daura and Waziri A. Gazali) Access to land under derived rights arrangement in Lake Alau, north eastern Nigeria. Maiduguri, Nigeria: Faculty of Social and Management Sciences, University of Maiduguri, 2000.
  1. 1.0 1.1 Rahaman Abiola (23 September 2020). "Abbah Tijani appointed as new NCMM DG". Legit.
  2. Gregory Austin Nwakunor (20 September 2020). "Experts set agenda for NCMM boss, Tijani". The Guardian.
  3. Vivienne Chow (29 October 2021). "After Years of Debate, Two Universities Have Become the First U.K. Institutions to Restitute Benin Bronzes".