Abba Kyari (ɗan sanda)
Abba Kyari (ɗan sanda) | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Maiduguri, 17 ga Maris, 1975 (49 shekaru) |
Sana'a |
Abba Kyari ( an haife shi a ranar 17 ga watan Maris, shekara ta 1975), Ya kasance sufeto janar ne na ’yan sanda da ke sashen hukumar a bangaren leken Asiri (IGP-IRT), sannan kuma mataimaki ne na kwamishinan yan sanda Ya kasance memba a gungiyar 'yan sanda na duniya wato (IACP), Kafin a kai ga naɗa shi a mukamin nasa na (IGP zuwa IRT), abba Kyari yayi aiki a ofishin ’yan sanda na Jihar Legas a matsayin Babban Jami’i mai kula da sashen yaki da ayyukan takadiranci (SARS).
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Abba Kyari ya shiga makarantar koyon aikin 'yan sanda da ke Wudil, jihar Kano a shekara ta (2000), Ya kammala karatunsa a matsayin karamin sufeto na 'yan sanda (ASP),inda aka tura shi zuwa ofishin 'yan sanda na jihar Adamawa. A nan ya shafe tsawon shekara guda bakin aiki a hedikwatar 'yan sanda na Song. Daga baya aka tura shi a matsayin jami'i na musamman a bangaren sashen hana miyagun laifuka na yanki (DCO), a Numan, jihar Adamawa. [1] Kyari ya kuma zama kwamandan sashin( 14 PMF), Yola.[2] Ya koma ofishin 'yan sanda na jihar Legas a matsayin (IC 2 ), sannan daga baya ya zama Jami'in-In-Caji na Sashin Sashin Yaki da' Yan Fashi da Makami (SARS), [3] Abba Kyari a halin yanzu Sufeto Janar na ‘Yan Sanda masu amsa bayanan sirri a cikin rundunar‘ Yan Sandan Najeriya hedi kwata a Abuja[4]
Tuhuma
[gyara sashe | gyara masomin]Hukumar Yan sanda ta Amurka (FBI),ta Kama shaharren Dan danfaran yanar gizo Wanda aka fi sani da Hushpuppy. Bayan an Kama shine yake bada bayanim cewa ya aikawa da dansan Dan Nigeria Abba Kyari da makudan kudade domin cin hanci Dan ya Kama abokin danfaran sa Dan wani sabani da suka samu. Wannan dalilin yasa Hukumar FBI take tuhumar Abba Kyari da cin hanci da rashawa da Kuma taimaka barayin yanar gizo.[5]
Wannan dalilin yasa Babban Spetan Yan sanda Nigeria (IGP), ya dakatar da Abba Kyari domin a samu daman Yin bincike cikakke game da tuhumar.[6]
Zargin sa da Kasuwancin Hodar Iblis
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 14 ga watan Fabrairu shekara ta 2022, an fallasa faifan bidiyon Abba Kyari inda aka ganshi yana kokarin sakin hodar Iblis mai nauyin kilo 25, aka ba da tsabar kudi dala $61,400.[7][8][9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Meet Deputy Commissioner Of Police, Abba Kyari: The Commander, IGP Intelligence Response Team (IRT)". Nigerian Voice. Retrieved 18 June 2020
- ↑ Akinnola, Richard (1 August 2021). "Nigeria's 3 major Abba Kyaris from Borno -". The Punch. Retrieved 1 August 2021.
- ↑ "CRIMINAL COMPLAINT BY TELEPHONE OR OTHER RELIABLE ELECTRONIC MEANS" (PDF). Peoples Gazette. Retrieved 1 August 2021.
- ↑ "Police IG Usman Baba suspends Abba Kyari over Hushpuppi multimillion-dollar fraud". Peoples Gazette.
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2021/07/how-hushpuppi-allegedly-bribed-abba-kyari-to-arrest-co-fraudster-in-1-1m-scam-us-report/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/476877-breaking-hushpuppi-igp-recommends-suspension-of-abba-kyari.html
- ↑ Oyero, Kayode (14 February 2022). "How Abba Kyari negotiated release of 25kg cocaine, offered $61, 400 cash –NDLEA". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 16 February 2022.
- ↑ Ibrahim, Salisu (14 February 2022). "Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa". legit.hausa.com. Retrieved 16 February 2022.
- ↑ "BREAKING: Police arrest Abba Kyari, 4 others". The Informant247.com. 14 February 2022. Retrieved 16 February 2022.
Hanyoyin hadin waje
[gyara sashe | gyara masomin]- CS1 Turanci-language sources (en)
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from September 2022
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- Rayayyun mutane
- Haifaffun 1975
- Jami'ar Maiduguri
- 'Yan Sandan Najeriya
- Mutane daga Jihar Borno
- Mutane daga Jihar Yobe
- Pages with unreviewed translations