Abd al-Rahim Abdul Rassak al-Janko
![]() | |
| Rayuwa | |
| Haihuwa |
Mardin (mul) |
| Mazauni |
Guantanamo Bay detention camp (en) |
| Sana'a | |
Abd al-Rahim Abdul Rassak al-Janko (عبدالرحیم عبدالرزاق الجنکو; an haife shi a shekarar 1977), ɗan ƙasar Suriya ne kuma Kurde. Tsohon ɗalibi ne a Ƙasashen Hadin Gwiwar Larabawa (UAE) wanda ya tafi zuwa Afghanistan a shekarar 2000.
A can ne kungiyar Taliban ta kama shi, inda suka bayyana cewa ya amince da laifin shirin kashe Usama Bin Laden, da kuma leƙen asiri a madadin Isra'ila da Amurka.[Ana bukatan hujja]
Haka kuma, an zarge shi da "lalatar jima’i da wasu samari" kuma aka tuhume shi da kasancewa ɗan luwadi.
Following the Invasion of Afghanistan, al-Janko begged a British journalist to alert the Americans that he had been held prisoner by the Taliban for two years; however, he was taken from the Taliban prison by American forces, and sent to the Guantanamo Bay detention camps where he spent seven years in detention.[1][2]
Lokacin da aka gano bidiyon tambayar al-Janko da aka yi masa a shekarar 2000 bisa zargin luwadi da leƙen asiri a kan Taliban[3] daga cikin ginin da Mohammed Atef ya baro, dakarun Amurka sun kwato shi daga rusasshiyar gida. Gwamnatin Bush ta saki bidiyon, inda aka nuna al-Janko yana kuka sosai, amma sai suka kakkaɓe sautinsa, suka kuma karya da cewa wannan bidiyo ne na "nema shahada" ko bidiyon shahada.
Sun ce wai al-Janko yana magana ne kan yadda zai mutu a matsayin shahidi, bayan mamayar Afghanistan da aka yi a 2001.
Ko da yake jami’an Amurka a cikin gida sun san gaskiyar bidiyon cewa tambaya ce da Taliban suka yi masa, gwamnati ta Amurka ta ci gaba da yi wa bidiyon lakabi da na “shahada” a fili, sannan ta saka sunan al-Janko cikin jerin FBI Seeking Information – War on Terrorism list.[1]
Amma maimakon a taimaka wa Ginco (al-Janko) ya koma gida, sojojin Amurka sun sake tsare shi. Bayan kusan shekara biyar, har yanzu yana tsare a gidan yarin sojin Amurka da ke Guantánamo Bay, Cuba — a wani bangare, bisa faifan bidiyon yaɗa farfaganda da masu azabtar da shi suka yi masa.
Amnesty International ta ƙalubalanci amfani da wannan bidiyon da ke nuna ana tambayar al-Janko da sunan hujja cewa yana da alaƙa da masu tayar da kayar baya, ta bayyana hakan a matsayin abin da ya kama da "kafkaesque" — wato abin da ke da wuyar fahimta kuma rashin adalci da kaskanci ne.[4]
Rayuwarsa kafin kamewa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi al-Janko a ƙasar Turkiyya, kuma shi ne ɗa na huɗu daga cikin yara goma sha ɗaya (11).[5]
Yana da shekaru huɗu kacal lokacin da sojojin Turkiyya suka kashe iyayensa ‘yan ƙabilar Kurdawa a shekarar 1980.
Bayan haka, iyayen aure suka ɗauke shi zuwa ƙasar Syria, inda ya zauna tsawon shekaru goma.
A shekara ta 1990, mahaifinsa na aure (wanda ya kasance Salafi) ya sami aikin malanta a Ajman, a cikin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). Bayan wasu shekaru, mahaifiyarsa ta aure da sauran ‘yan uwansa suka koma gare shi a Ajman.[Ana bukatan hujja]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Tim Golden (2006-10-15). "Expecting U.S. Help, Sent to Guantánamo". The New York Times. Retrieved 2010-07-27.
Mr. Ginco, a college student living in the United Arab Emirates, had gone to Afghanistan in 2000 after running away from his strict Muslim father. He was soon imprisoned by the Taliban, and tortured by operatives of Al Qaeda until, he said, he falsely confessed to being a spy for Israel and the United States.
- ↑ OARDEC (May 15, 2006). "List of Individuals Detained by the Department of Defense at Guantanamo Bay, Cuba from January 2002 through May 15, 2006" (PDF). United States Department of Defense. Archived from the original (PDF) on 30 September 2007. Retrieved 2007-09-29.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>tag; no text was provided for refs namedTimes2009-01-16 - ↑ Parker, Tom, "Obama Embracing Bush Legacy Archived 2012-03-09 at the Wayback Machine," Human Rights Now Blog, 1 Yuli 2009.
- ↑ Collingsworth, Terrence P.; Green, Jennifer M.; Hoffman, Paul L.; Brown Chomsky, Judith (October 5, 2010). "Abdul Rahim Abdul Razak al Janko: Complaint for Damages". Center for the Study of Human Rights in the Americas. UC Davis.
