Abdul-Malik al-Houthi
![]() | |||
2004 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa |
Saada Governorate (en) | ||
| ƙasa |
Yemen Republic (en) | ||
| Ƴan uwa | |||
| Mahaifi | Badreddin al-Houthi | ||
| Ahali |
Abdul Khaliq Al-Houthi (en) | ||
| Karatu | |||
| Harsuna | Larabci | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Aikin soja | |||
| Ya faɗaci |
Houthi insurgency (en) | ||
| IMDb | nm16370939 | ||
Abdul-Malik Badr al-Din al-Houthi (an haife shi a ranar 22 ga Mayu 1979) ɗan siyasan Yemen ne kuma shugaban addini wanda shi ne shugaban Houthis (Ansar Allah) na biyu, ƙungiyar da galibi ta ƙunshi Musulmi 'yan Shi'a, tun 2004.
'Yan uwansa, Yahia da Abdul-Karim suma shugabannin kungiyar ne, haka ma 'yan uwansa Hussein, Ibrahim, da Abdulkhaliq. Abdul-Malik al-Houthi shi ne jigo a yakin basasar Yaman wanda ya faro tun lokacin da 'yan Houthi suka mamaye kasar Yaman a yankin Sa'ada da ke arewacin kasar Yemen.
Rayuwar sirri
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Al-Houthi a gundumar Saada, Jamhuriyar Larabawa ta Yemen, a cikin kabilar Houthi a ranar 22 ga Mayu 1979.[1][2]Shi dan Shi'a Zaydi ne. Mahaifinsa, Badreddin al-Houthi, malamin addini ne na tsirarun kungiyar Zaydi ta Yemen. Abdul-Malik shi ne auta a cikin ‘yan uwansa takwas[3]. Babban yayansa Hussein ya kasance dan siyasa kuma dan majalisar dokokin kasar Yemen, haka nan kuma ya kasance fitaccen[4] mai sukar tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh. Husaini ya kafa kungiyar Houthi ne don inganta tunanin Zaidi, "tashi kan azzalumai da ke mulkin Yemen", da kuma samar da ayyukan ilimi da zamantakewa. Bayan kashe Husaini, Abdul-Malik ya gaje shi ta hanyar karbe iko da kungiyar Houthi.[6][7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Abdul Malik Al Houthi: The Shiite Thorn on Yemen's side". www.albawabaeg.com. Archived from the original on 18 May 2015. Retrieved 27 April 2015.
- ↑ "Yemen's Abd-al-Malik al-Houthi". BBC. Archived from the original on 2 March 2015. Retrieved 29 April 2015.
- ↑ Finn, Tom (13 February 2015). "Abdel-Malek al-Houthi: from shadow rebel leader to kingmaker". Middle East Eye. Retrieved 27 April 2015.
- ↑ "Brother of Houthis' top leader believed dead after air strike". The National. 1 September 2018. Retrieved 14 May 2020.
