Jump to content

Abdulbaqi Aliyu Jari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulbaqi Aliyu Jari
Rayuwa
Haihuwa 18 ga Augusta, 1991 (32 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan jarida da maiwaƙe
Abdulbaqi a ranar Hausa ta duniya
abdulbaqi maaikacin BBC
hoton abdulbaqi aliyu jari

Abdulbaqi Aliyu Jari (An haife shi a ranar goma sha takwas 18 ga watan Agustan, shekara ta alif ɗari tara da casa'in da ɗaya 1991). Akan rubuta shi da Abdulbaki Aliyu Jari kuma akan kira shi da Bahaushe, dan Najeriya ne, dan jarida, marubuci, mai fafutuka ne a kafar sada zumunta[1][2]. Shi ne wanda ya kafa Ranar Hausa, ranar da aka ware domin bikin yaren Hausa[3][4]. Shi ne kuma wanda ya kirkiro IHAME sabuwar alama ta rubuta harshen Hausa[5]. Shi ne tsohon shugaban sashen Hausa na Naija News Media kuma tsohon mataimakin editan gidan talabijin na Nishadi[6].

Farkon rayuwa da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Abdulbaqi an haife shi kuma ya girma a jihar Katsina, ya samu digiri na farko daga jami'ar Usman Danfodio Sakkwato a Biochemistry. Ya kuma sami difloma a Kimiyyar Computer da kuma Shari'a. Bayan kammala karatunsa daga Jami’ar Usman Danfodio, Abdulbaki ya fara aikinsa na dan Jarida mai zaman kansa, ya rubuta labarai sama da guda dubu daya 1,000 wanda jaridu sama da guda dari 100 suka buga wadanda suka hada da Daily Trust, BBC Hausa, Legit.ng. Shi ne tsohon Shugaban sashen Hausa na Naij News kuma daga baya ya zama Mataimakin edita a gidan talabijin na Nishaɗi. Abdulbaqi a halin yanzu mai gabatar da bidiyo ne tare da BBC[7][8]. Ya gudanar da bincike tare da African Eye na BBC inda ya kasance daga cikin wanda suka yi bincike a cikin shirin Tabay Torture Technique da Fake News.

A shekarar alif dubu biyu da goma sha daya 2011, Abdulbaqi ya kirkiri alamomin rubutun Hausa wadda ake kira Ihame. Ihame ya kunshi haruffan Hausa, adadi da kuma hanyar rubutu, ya yi shekara ukku 3 yana bincike sannan ya kammala aikinsa. Tare da taimakon Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, an buga Ihame a cikin mujallu ukki 3. Yanzu haka ana inganta Ihame ga mutanen Hausa. A cikin ashirin da shida 26 ga watan Agusta shekara ta alif dubu biyu da goma sha biyar 2015, Jari ya kafa Ranar Hausa ta duniya, ya fara gabatar da bikin farko a kafafen sada zumunta musamman ta shafin twitter da niyyar hada L1 da L2 na masu magana da harshen Hausa. Yayin bikin shekara biyar 5, mutane fiye da dubu dari hudu 400,000 suka halarci duka ta yanar gizo kuma an gudanar da bikin a Faransa, Amurka, Kamaru, Ghana, Nijar, da Najeriya Saboda gudummawar da ya bayar ga Hausawa, marigayi Sarkin Rano ya ba shi Abdulbaqi lakabi na gargajiya na Sarkin Yakin Hausa[9]. (Chief Publicist of Hausa) daga wajen sarkin Kano Emir of Rano.

Abubuwan sasantawa gwagwarmayar zamantakewa

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta dubu biyu da goma sha hudu 2014, Jari ya la'anci matakin da gwamnatin jahar Legas ta ɗauka na hana 'yan matan musulmai sanya Hijabi a makaranta.[10] Jari yana cikin wadanda suka matsa lamba ga gwamnan jahar Katsina a cikin Shekara ta alif dubu biyu da goma sha hudu 2014 don sakin wani ɗalibi da aka tsare saboda wani shafin Facebook.[11]

Wasu labarai da aka zaba da kuma binciken Abdulbaki Jari

[gyara sashe | gyara masomin]
 • Kisan Kenya da kuma aikin watsa labarai na duniya
 • Shugaba Janatan ya “yi tambayoyi”
 • Shugaban arewa ya dauki alhakin matsalolinmu
 • Dalilin da ya sa aure tsakanin mutanen Hausawa yakan gaza
 • Xenophobia da hadin kan Afirka
 • Ina tauraron mu guda hudu.
 1. Mustapha, Mallam. "Personality of the week: Commrade Abdulbaqi Aliyu Jari". Katsina Post. Archived from the original on 24 June 2020. Retrieved 21 June 2020.
 2. Akinola, Wale (31 March 2017). "Young Hausa-Fulani poet's call for division of Nigeria, sparks reactions". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 21 June 2020.
 3. "Hausa Day takes center stage in cyberspace". FRCN. 26 August 2018. Archived from the original on 28 June 2020. Retrieved 25 June 2020.
 4. "The story of #HausaDay and how it is uniting people". CliqqMagazine. 19 June 2020. Archived from the original on 23 June 2020. Retrieved 21 June 2020.
 5. "Ihame: Hausa alphabets, numerals on invention". www.pressreader.com. Retrieved 21 June 2020.
 6. "The Media 100 2020 list, the culture curators, the fourth estate". YNaija. 22 May 2020. Retrieved 21 June 2020.
 7. "TEDxYouth@Barnawa | TED". www.ted.com. 22 May 2020. Retrieved 21 June 2020.
 8. "#MANCRUSHMONDAY – Tozali Online". Tozali online. Retrieved 21 June 2020.
 9. "The story of #HausaDay and how it is uniting people". Katsina Post. Archived from the original on 21 June 2020. Retrieved 21 June 2020.
 10. "4 Reasons Why Fashola Must 'Bring Back Our Hijab' — Student". Pulse Nigeria. 19 October 2014. Retrieved 25 June 2020.
 11. "Gov Shema Urged to Release Student Arrested For Criticising Him". Prompt News. 24 September 2014. Archived from the original on 25 June 2020. Retrieved 25 June 2020.

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]