Jump to content

Abdulkadir Aliyu Mahe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulkadir Aliyu Mahe
Rayuwa
Haihuwa Ilorin, 1951
ƙasa Najeriya
Mutuwa Ilorin, 28 Disamba 2024
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Yarima Abdulkadir Aliyu Mahe (1951 - 28 Disamba 2024) ɗan siyasan Najeriya ne kuma sakataren gwamnatin jihar Kwara kuma shugaban ma'aikata na gwamnan jihar Kwara Mallam AbdulRahman AbdulRazaq har zuwa rasuwarsa. [1] [2]

Rayuwa da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mahe a shekarar 1951 a Ilorin, karamar hukumar Ilorin ta kudu a Jihar Kwara, kasar Najeriya. Ya karanta Business Administration a Jami'ar Calabar, inda ya samu digiri na biyu. Bugu da kari, ya samu takardar shaidar kammala difloma ta kasa(ND) da kuma babbar difloma(HND)a fannin kasuwanci daga Kaduna Polytechnic da kuma Kwara State Polytechnic, bi da bi. [2]

A watan Satumbar 2023, an zaɓi Mahe a matsayin sakataren gwamnatin jihar Kwara, mukamin da ya rike kafin a nada shi a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kwara, Mallam AbdulRahman AbdulRazaq. Mahe, wanda ya kasance sakataren dindindin wanda yayi ritaya, ya kuma taba zama tsohon magatakarda a majalisar dokokin Jihar Kwara. [2] [3] [4]

Mahe ya mutu a ranar 28 ga watan Disamba, 2024. [5]

  1. "Sallah: Kwara Gov prays for peace, progress for Nigeria – Daily Trust". dailytrust.com. Retrieved 28 December 2024.
  2. 2.0 2.1 2.2 Nwafor (4 September 2023). "Kwara Gov names Prince Mahe new SSG, inaugurates cabinet". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 28 December 2024.
  3. Azeez, Biola (23 September 2024). "Kwara governor swears in newly elected council chairmen". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 28 December 2024.
  4. Azeez, Biola (28 December 2024). "Gov Abdulrazaq's Chief of Staff is dead". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 28 December 2024.
  5. Olesin, Abdullahi (28 December 2024). "Kwara Gov's Chief Of Staff, Prince Mahe, Dies" (in Turanci). Retrieved 28 December 2024.