Jump to content

Abdulrahman Kuliya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulrahman Kuliya
Rayuwa
Haihuwa 1968
Mutuwa 2021
Sana'a

Birgediya Janar Abdulrahman Kuliya (An haife shi ranar 2 ga watan Fabrairu, 1968 – 21 ga watan Mayu, 2021) ya kasance jami'in soja na Najeriya.[1][2][3] Ya rasu a hatsarin jirgin saman soja tare da Shugaban Hafsan Sojojin Kasa (COAS) Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami'an soja 9 a kan aiki.[4][5]

Ya hau zuwa matsayin Birgediya Janar a Rundunar Sojan Najeriya. Ya rike mukamai da dama a lokacin aikinsa ciki har da Darakta, Yakin Kasa a Kwalejin Kwamando da Ma’aikatan Sojoji. Kuliya ya kasance Shugaban Sashen Leken Asiri na Sojoji – Rundunar Leken Asiri ta Sojan Najeriya har zuwa rasuwarsa a ranar 21 ga Mayu, 2021.

  1. "Abdulrahman Kuliya Archives". TheCable. Archived from the original on 27 May 2021. Retrieved 27 May 2021.
  2. "EXCLUSIVE: Major shake-up as Army redeploys 120 generals, others [FULL LIST]". Premium Times. 6 March 2021. Retrieved 26 May 2021.
  3. "Buratai appoints new Operation Lafiya Dole commanders". Punch Newspapers. 6 December 2018. Retrieved 26 May 2021.
  4. "Ceaseless rain of tributes for departed officers". The Guardian Nigeria News. 23 May 2021. Retrieved 26 May 2021.
  5. "Biography of di officers wey die for military plane crash wit Chief of Army Staff". BBC News Pidgin (in Pidgin na Najeriya). Retrieved 26 May 2021.