Jump to content

Abdulwaheed Ofolabi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abdulwaheed Afolabi

Abdulwaheed Afolabi (an haife shi a ranar 8 ga Disamba 1991) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Najeriya wanda ke buga wa ƙungiyar Loto-Popo FC ta ƙasar Benin. Abdulwaheed ya buga wa ƙungiyar Russian Premier League, Kuban Krasnodar, da kuma ƙungiyar Ukraine Premier League, Tavriya Simferopol. Ya buga wasanni 14 kuma ya zura kwallaye 3 a ƙungiyoyin matasa na ƙasar Najeriya.

AIKINSA

Afolabi ya shiga gwaji tare da Black Leopards na Gasar Premier ta Kwallon Kafa ta Afirka ta Kudu a watan Agustan 2011, amma tattaunawa ta rushe kuma ya koma Niger Tornadoes.[1] A watan Maris na 2012, Afolabi ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu tare da kungiyar Tavriya Simferopool ta Ukraine.[2] Daga nan Afolabi ya koma kungiyar Rasha ta Premier League, Kuban Krasnodar a watan Agustan 2012, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru hudu. Afolabi ya fara buga wasa na farko ga Kuban a ranar 30 ga Nuwamba 2012 a wasa da FC Krasnodar.

'''Manazarta'''

  1. https://en.wikipedia.org/wiki/Abdulwaheed_Afolabi#cite_note-1
  2. https://en.wikipedia.org/wiki/Abdulwaheed_Afolabi#cite_note-2