Abdur-rahman ibn abubakar atiku

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Abdur-rahman ibn abubakar atiku An haife shi ne a Wurno a cikin shekara 1828 ko 1829.Kalifa Abdurrahman yana cikin Kalifofin a tarihin Sokoto wanda labarin shi ya samu tsaiko da rashin fahimta. Yazo daga bakin turawa wa inda suka karance shi cewa lokacin Kalifa Abdurrahman, lokaci ne na yaki, zalinci da azaba. Jin hakan yasa mafi yawan mutane suke danganta Kalifa Abdurrahman a matsayin wanda ya gaza ko kuma wanda ba’a sani ba a cikin Kalifofi.[1]

Karatu[gyara sashe | Gyara masomin]

An samu rashin daidaito akan takamaiman malamin da ya fara karantar da Kalifa abdurrahman a farkon rayuwarsa. Amma anfi ganin cewa mahaifinsa shine farkon malaminsa. Sannan kuma da mahaifiyarsa. Daga bisani yayi karatu a karkashin lokacin Kalifa bello. Inda wa innan malaman suke a sokoto, salame da wurno. An rawaito cewa Kalifa abdurrahman ya iya karatun kur’ani a kankanin shekarun sa.

Sarauta[gyara sashe | Gyara masomin]

Rasuwatr Kalifa umar ta bada damar nada wani Kalifa kamar yadda musulunci ya tanada. Duba da cewa lokacin, lokacin yaki ne wannan dalilin yasa ba’a tsaya yin tanaji da akayi mai tsawo ba wajen zaben Kalifa, inda aka kira, abdurrahman da daniya ibn rufa’i. Inda daniya da karshe yayi ma abdurrahman mubaya’a. Sannan aka bada shawarar ayi amfani da masallacin kaura domin nadashi Kalifa. An nada abdurrahman a masallacin kaura a matsayin khalifa a shekara 1891, march ranar laraba. Sa’i kadan bayan rasuwan umar.[1]

Rasuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

Lokacin da Kalifa abdurrahman ya lura cewa, kwana kin sa a duniya sun kusa karewa. Sai ya kobe kansa a cikin gidansa. Sannan yabar jagoranci ga Wazirin sa, inda ya bukaci kada a fito dashi inba ya zama dole ba. Ya killace kansa ne da Al-Qur’ani da wuka.[1]

Bibiliyo[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. ISBN 978-978-956-924-3. OCLC 993295033.
  • The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.
  • Smaldone, Joseph P. (1977). Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. p.p 193-214 ISBN 978-978-956-924-3.