Jump to content

Abincin Mutanen Yukren

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abincin Mutanen Yukren
national cuisine (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Ukrainian culture (en) Fassara
Al'ada Ukrainian culture (en) Fassara
Ƙasa Ukraniya
Ƙasa da aka fara Ukraniya
Kayan abinci na Ukrainian daga gidan cin abinci na zamani a Lviv

  Abincin Mutanen Yukren shine tarin al'adun dafa abinci daban-daban na mutanen Ukraine, ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Turai kuma mafi yawan jama'a. Kasar ta tasirantu da kasar shuka mai mai duhu mai arzikin noma (chornozem) daga inda sinadarai ke fitowa, kuma sau da yawa ya haɗa da abubuwa da yawa.[1] Kayan abincin gargajiya na Yukren sau da yawa ana dafa su sosai - "da farko ana fara soya su ko tafasa su, sannan ayi miya da su ko a gasa su. Wannan shine salon girka kayan abincin Yukren da yawa.[2]

Abincin mutanen kasar Ukraine shine ja Borscht, sanannen miyan beet, wanda akwai nau'o'i iri-iri. Koyaya, varenyky (gurasa mai kama da pierogi) da kuma wani nau'in kabeji da aka sani da holubtsi su ne kayan abincin da aka fi so a ƙasan, kuma abinci ne na yau da kullun a gidajen cin abincin gargajiya na kasar Yukren.[3] Wadannan kayan abinci suna nuna kamanceceniya a nau'in kayan abinci irin na mutanen Gabashin Turai.

Abincin yana jaddada muhimmancin musamman alkama, da hatsi gabaɗaya, kamar yadda ake kiran ƙasar "kwandon burodin Turai".[4] Yawancin abincin Ukrainian sun fito ne daga kayan abinci na manoma na dā wanda ya dogara da albarkatun hatsi masu yawa kamar rye, da kuma kayan lambu masu mahimmanci kamar dankali, kabeji, mushroom da beetroots. Abincin mutanen Yukren ya haɗa da salon girkin gargajiya na Slavic da sauran dabaru na Turai, sakamakon dumbin shekaru na mulkin mallaka da tasiri na kasashen waje. Kamar yadda ya kasance da watsuwar mutanen Yukren na tsawon karni da yawa (alal misali, sama da 'yan Kanada miliyan ɗaya sun fito ne daga tsatson mutanen Yukren), ana amfani da ire-iren abincin a ƙasashen Turai da waɗanda ke nesa, musamman Argentina, Brazil, da Amurka.

 

Abinci na zamani na ƙasashen Ukraine na zamani

[gyara sashe | gyara masomin]
Yin shayarwa na kissel a Belgorod (Bilohorodka ta zamani), ƙarami daga Tarihin Radziwiłł .
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


  1. "Food in Ukraine – Ukrainian Food, Ukrainian Cuisine – traditional, popular, dishes, recipe, diet, history, common, meals, staple". www.foodbycountry.com.
  2. "Ukrainian National Food and Cuisine". ukrainetrek.com.
  3. "5 Best Ukraine traditional Foods". Archived from the original on 14 August 2013.CS1 maint: unfit url (link)
  4. "The Bread Basket of Europe". InfoPlease.