AdSense

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Google AdSense wata manhajar Google ce da ke barin mawallafa a cikin Cibiyar Google ta shafukan yanar gizo su iya bada tallace-tallacen da aka rubutu, ko hotuna, ko bidiyo, ko tallan da za a iya hulɗa da su, duk ta hanya mai sauƙi kuma atomatik, waɗanda aka yi niyyar su je ga masu ziyarar shafin. Kamfanin Goolge ne mai kula, mai tantance, da tafiyad da waɗannan tallan. Suna iya samar da kuɗaɗan shiga ta hanyar danna tallan (per-click) ko idan an nuna tallan (per-impression). A farkon kwatar shekara 2014, Google ta sami bilyon $3.4 (wato bilyon $13.6 a gabaɗayar shekarar), ko kashi 22 cikin ɗari a adadin kuɗaɗan shiga na Google ta hanyar Google AdSense.[1] Sama da shafuka miliyan 14 ne ke amfani da AdSense.[2]

References[gyara sashe | Gyara masomin]