Adam A Zango
|
| |
| Rayuwa | |
| Haihuwa | Zango, 1 Oktoba 1985 (40 shekaru) |
| ƙasa | Najeriya |
| Harshen uwa | Hausa |
| Karatu | |
| Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
| Sana'a | |
| Sana'a | jarumi, mawaƙi, mai rawa da marubin wasannin kwaykwayo |
| Imani | |
| Addini | Mabiya Sunnah |





Adam A Zango
Adam A. Zango (Taimako·bayani) Dan wasan kwaikwayo ne na Najeriya, mawaki, dan rawa, marubuci, darakta, mai shirya fina-finai na Hausa, dan shirin talabijin, kuma mai taimakon jama'a. Ya fito a fina-finai sama da guda dubu daya (1000) kuma ya samu lambar yabo da yawa. Adam A. Zango yana da dimbin mabiya a Afirka da ma sauran kasashen Najeriya da Nijar a duniya. Dangane da lambobin fina-finan da aka nuna da sassaucin ra'ayi, an bayyana shi a matsayin jarumin fina-finan da sukayi fice a Afrika, kuma shahararren mai bada nishadin Hausa a duniya. Acikin shekarar 2000, ya kasance babban jarumi a fagen fina-finan Hausa. Adam A Zango yana samun labarai da yawa na kafofin watsa labarai a Najeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Chadi, Togo da Benin, kuma galibi ana kiransa da “Yariman kowane lokaci” Shi ne abin da wasu masu kishin addini ke bi, wani lokaci tushe an kiyasta ya zarce miliyoyi kuma ana kiransa" babbar tauraruwar Hausa a duniya". Dangane da binciken shaharansa,
Sama da mutane miliyan dari uku (30,000) a duk duniya suka san Adam A. Zango. Yana daya daga cikin masu nishadantarwa mafi girma a Najeriya kuma daya daga cikin shahararrun mashahuran mutane a tallan talabijin. Adam A. Zango ya kasance jakadan kamfen na gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu a kasar Najeriya baki daya.[1]
Haihuwa.
[gyara sashe | gyara masomin]Adam Abdullahi Zango, an haife shi a watan Oktoba, na shekara ta alif da dari tara da tamanin da biyar (1985). Miladiyya. a karamar hukumar Zangon kataf,a jihar Kaduna, Najeriya da ga Malam Abdullahi da kuma Hajiya Yelwa Abdullahi, yan kabilan, Hausa kuma mabiya addinin Musulunci.[2]
Sana'a.
[gyara sashe | gyara masomin]Adam A. Zango ya fara aikin kira ne daga ayyukan makarantar sakandare wanda ke jagorantar kwanakin/bukukuwan kulob din da ya kasance yana wakiltan makarantarsa a makarantar sakandire ta gwamnati laranto jos Jihar Filato. Adam A. Zango ya fara shiga harkar fim din Hausa a shekara ta dubu biyu da daya (2001) a matsayin mawaki. Ya fara sana'ar wasan kwaikwayo a matsayin karamin dan wasan kwaikwayo kuma ya fito a fina-finan Hausa ku san sama da guda dari (100).
Karatun sa
[gyara sashe | gyara masomin]Adam A. Zango ya fara karatun firamare a shekarar alif da dari tara da tamanin da tara (1989) zuwa shekara ta dubu daya da dari tara da casa'in da biyar (1995), miladiyya. Ya fara sakandire daga shekarar alif da dari tara da casa'in da shidda (1996) zuwa shekarar dubu biyu da daya (2001). Adam A. Zango be cigaba da karatu ba, bisa ra'ayinsa na cewa ba dole sai kayi karatu zaka iya zama wani abinda da zaka taimaki al'umma ba.[3]
Wakoki
[gyara sashe | gyara masomin]- Wasu Daga Cikin Wakokin Adam A Zango Archived 2022-02-12 at the Wayback Machine
- Duniya tazo karshe
- Wakan sarkin zazzau
- Shahuda
- Samarin duniya
- Komai daga Allah ne
- Tsumagiya
Gudummawar da yabada ga alumma
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Oktoba na shekara ta dubu biyu da sha tara (2019), Adam A Zango Ya biya, a matsayin sadaqa, da Naira miliyan arba'in da bakwai (47,000,000) Naira ga yara, marayu, domin ci gaba da karatu. An yi haka a fadar Shehu Idris Sarkin Zazzau.[4]
Aure
[gyara sashe | gyara masomin]Adam A. Zango yayi aure akalla shidda (6), yana rabuwa da matan. yanada Yara guda bakwai shida daga Matan da ya aura guda biyar. Sai daya daga wacce ya aura ta karshe ta haifi diya mace. Sunan babban dansa Aliyu haidar.

Filmography
[gyara sashe | gyara masomin]| Film | Year |
|---|---|
| 'Ya'Yana | ND |
| 'Yar Agadez | 2011 |
| Adamsi | 2011 |
| Addini ko Al'Ada | 2011 |
| Adon Gari | 2011 |
| Ahlul Kitabi | 2011 |
| Alkawari na | 2011 |
| Albashi (The Salary) | 2002 |
| Andamali | 2013 |
| Ango da Amarya | ND |
| Artabu | 2009 |
| Aska Tara | ND |
| Auren Tagwaye | ND |
| Baban Sadik | 2012 |
| Babban Yaro | 2011 |
| Balaraba | 2010 |
| Basaja | 2013 |
| Bayan Rai | 2014 |
| Bita Zai Zai | ND |
| Dajin So | ND |
| Dan Almajiri | ND |
| Dare | 2015 |
| Dijangala | 2008 |
| Duniya Budurwar Wawa | ND |
| Dutsen Gulbi | 2013 |
| Farar Saka | ND |
| Fataken Dare | ND |
| Ga Duhu Ga Haske | 2010 |
| Ga Fili Ga Mai Doki | ND |
| Gaba da Gabanta | 2013 |
| Gambiza | ND |
| Gamdakatar | ND |
| Gwamnati | 2003 |
| Gwanaye | 2003 |
| Gwaska | 2016 |
| Hadizalo | ND |
| Hindu | 2014 |
| Hisabi | 2017 |
| Hubbi | 2012 |
| Ijaabaah | ND |
| Jamila | 2016 |
| Kaddara Ko Fansa | 2014 |
| Kama da Wane | 2014 |
| Kare Jini | ND |
| Kolo | ND |
| Kundin Tsari | ND |
| Laifin Dadi | 2010 |
| Larai | ND |
| Madugu | ND |
| Masu Aji | ND |
| Mata ko Ya | 2015 |
| Matsayin So | ND |
| Mazan Fama | ND |
| Matsayin So | ND |
| Mazan Fama | 2015 |
| Mukaddari | ND |
| Murmushin Alkawari | ND |
| Mutallab | 2011 |
| Nai Maka Rana | ND |
| Namamajo | ND |
| Nas | 2013 |
| Ni Da Ke Mun Dace | 2013 |
| Najeriya Da Nijar | 2012 |
| Nusaiba | ND |
| Rabin Jiki | 2011 |
| Rai A Kwalba | ND |
| Rai Dai | 2012 |
| Rawar Gani | ND |
| Rintsin Kauna | ND |
| Rumana | 2017 |
| Ruwan Ido | ND |
| Ruwan Jakara | ND |
| Sai Wata Rana | 2010 |
| Salma | ND |
| Shahuda | 2012 |
| Siyayya Da Shakuwa | 2014 |
| Soyayyar Facebook | 2013 |
| Tarkon Kauna | ND |
| Tsangaya | ND |
| Ummi da Adnan | 2011 |
| Walijam | 2010 |
| Wata Rayuwa | 2013 |
| Ya Salam | ND |
| Zanen Dutse | ND |
| Zarar Bunu | 2011 |
| Zatona | ND |
| Zeenat | 2014 |
| Zo Mu Zauna | ND |
| Zullumi 2017 | |
Asin da Asin film mai dogon zango}
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
Hanyoyin hadi na waje[gyara sashe | gyara masomin] |
- Mukaloli masu sauti
- All articles with unsourced statements
- Articles with unsourced statements from May 2021
- Articles with invalid date parameter in template
- Webarchive template wayback links
- Rayayyun mutane
- Hausawa
- Yan wasan kwaikwayo
- Maza yan wasan kwaikwayo
- Haifaffun shekarar dubu daya da dari Tara da tamanin da biyar miladiyya1985
- Mutane daga jihar kaduna