Jump to content

Adama Diatta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adama Diatta
Rayuwa
Haihuwa Kabrousse (en) Fassara, 14 ga Augusta, 1988 (35 shekaru)
ƙasa Senegal
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a amateur wrestler (en) Fassara
Nauyi 57 kg
Tsayi 165 cm

Adama Diatta (an Haife shi ranar 14 ga y Agustan 1988) ɗan kokawa ne na ƴanci kuma ɗan Senegal. Ya halarci gasar tseren kilo 55 na maza a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2008. A zagaye na 16, ya yi rashin nasara a hannun Tomohiro Matsunaga daga Japan. A zagayen sake fafatawa, ɗan ƙasar Turkiyya Sezar Akgul ya doke shi.

Ya yi takara a Senegal a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2016 a cikin 57 kg rabo.[1] Yowlys Bonne na Cuba ya doke shi a zagayen farko. Shi ne mai riƙe da tutar Senegal a lokacin rufe gasar.[2]

Ta hanyar gasar Kokawa ta Afirka da Oceania ta shekarar 2021, ya sami cancantar wakiltar Senegal a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2020 a Tokyo, Japan.[3][4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]