Adebisi Akande

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adebisi Akande
Gwamnan Jihar Osun

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2003
Theophilus Bamigboye (en) Fassara - Olagunsoye Oyinlola
Rayuwa
Haihuwa Ila Orangun, 23 ga Janairu, 1939 (85 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yarbawa
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Alliance for Democracy (en) Fassara

Abdukareem Adebisi Bamdele Akande ("Bisi Akande"; an haife shi a ranar 16 ga watan Janairu shekara ta 1939) shi ne gwamnan jihar Osun, Nijeriya daga shekara ta (1999 zuwa 2003) a matsayin memba na jam'iyyar Alliance for Democracy (AD), kuma shi ne Shugaban riko na farko na All Progressives Congress.

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Cif Adebisi Akande an haife shi a Ila Orangun a ranar 16 ga watan Janairun shekara ta 1939 a yankin da ake kira Osun Central Senatorial a yanzu. An zabe shi ne a kan dandalin Unity Party of Nigeria (UPN). An bayyana Akande a matsayin dan wa ga Cif Bola Ige.

Aikin gwamna[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓi Akande a matsayin gwamnan jihar Osun a watan Afrilun shekara ta (1999) yana takarar jam’iyyar Alliance for Democracy (AD), wacce a baya-bayan nan ta kafa kungiyar siyasa ta kungiyar yarbawa ta Afenifere. Ya gaji Kanar Theophilus Bamigboye, wanda aka nada a matsayin mai kula da mulkin soja na jihar a watan Agustan shekarar (1998) wanda kuma ya mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu a shekara ta (1999) A ranar 31 ga watan Mayu a shekara ta (1999) Akande ya kaddamar da majalisa ta biyu a jihar Osun.

Akande ya sake tsayawa takara a shekarar (2003) amma Prince Olagunsoye Oyinlola na jam’iyyar People's Democratic Party (PDP) ya kayar da shi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://web.archive.org/web/20110724235004/http://www.alliancefordemocracyusa.org/prelease.htm