Jump to content

Ado Aleru

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ado Aleru
Rayuwa
Sana'a

Ado Aleru wanda aka fi sani da Adamu Aliero sanannen shugaban ƴan-fashi ne da ke ta'addancinsa a yankin arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihohin Zamfara da Katsina. Ana danganta shi da hare-hare masu yawa, satar mutane, da satar shanu a cikin shekaru da yawa.

Naɗin Sarauta

[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Yulin 2022, Sarkin Ƴandoto Daji a Jihar Zamfara, Aliyu Marafa, ya ba Aleru sarautar "Sarkin Fulani" (Shugaban Fulani). Bayar da sarautar kamar wani ɓangare ne na yarjejeniyar zaman lafiya don rage tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya.Wannan yunkurin ya haifar da ce-ce-kuce da fushin jama'a a ƙasa baki ɗaya, kamar yadda mutane da yawa suka nuna cewa bai kamata a girmama mai laifi da wata sarauta ba hasali ma hukuma na nemansa ruwa a jallo wai. Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin.Duk da wannan, wasu shugabannin yankin sun kare yunƙurin, suna masu cewa yin hakan ya rage rikice-rikice na ɗan lokaci a yankin.

Taron Zaman Lafiya tare da Al'ummar wani yaki a Katsina

[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Yunin 2025, Aleru ya halarci taron zaman lafiya a Danmusa, Katsina. Ya nema zauna a tattaunawa, sai dai ya ƙi amincewa da cewa an kira su ƴan'ta'adda ne, kuma ya ce ƴan fashi ma suna da nasu korafe-korafen. Taron ya haifar da ce-ce-kuce tsakanin jama'a kasancewar har zuwa lokacin wai hukuma tana nemansa . Bayan kammala taron Aleru ya ce "Idan har yanzu ana kiran mu ƴan'ta'adda, to kada ayi zaton zamu daina nuna halin ƴan'ta'adda" [1]

Matsayin Hukuma akan Nemansa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya kasance a cikin jerin waɗanda take mena ruwa a jallo wai, wanda haɗa kuɗi Naira miliyan biyar aka sanya ga duk wanda ya kawo shi koda rai ko a mace, bayan taron hukumar ƴansanda reshen jihar Katsina ta bayyana har yanzu shi abin nema ne kuma suna nan a matsayar su.

  1. Makama, Zagazola (14 June 2025). "Ado Aleru: "If we are still being called terrorists, don't expect us to stop the violence"". zagazola.org. Retrieved 19 August 2025.