Affoussiata Bamba-Lamine
|
| |||
21 Disamba 2012 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Abidjan, 23 ga Yuni, 1970 (55 shekaru) | ||
| ƙasa | Ivory Coast | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
Université de Paris (mul) Nancy-Université (mul) | ||
| Harsuna | Faransanci | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa da minista | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa |
Rally of the Republicans (en) | ||
Affoussiata Bamba-Lamine (an haife ta a ranar 23 ga watan Yuni 1970) 'yar siyasar ƙasar Ivory Coast ce wacce ta yi aiki a matsayin Ministar Sadarwa daga watan Disamba 2012 har zuwa watan Janairu 2017.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Bamba-Lamine a ranar 23 ga watan Yuni 1970 a Abidjan. Mahaifinta, Moriféré Bamba, shi ne Ministan Sadarwa a lokacin wa'adin Alassane Ouattara. Tana da digiri na shari'a daga Jami'ar Robert Schuman a Strasbourg, digiri na biyu a fannin shari'a daga Jami'ar Paris X da digiri na uku a fannin shari'a daga Jami'ar Nancy 2 a Faransa. [1]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Bamba-Lamine ta yi doka a Faransa, ta zama memba na Bar a Paris a shekarar 2001.
A cikin shekarar 2002, Bamba-Lamine ta zama mai ba da shawara kan harkokin shari'a a ma'aikatar sadarwa, kuma ta yi aiki a ofishin Firayim Minista daga shekarun 2007 zuwa 2012. A lokacin rikicin 2010–11 na Ivory Coast, ta shiga cikin Forces Nouvelles kuma ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan doka ga Guillaume Soro. [2] [3]
An zaɓi Bamba-Lamine a matsayin ɗan majalisar wakilai ta ƙasa na gundumar Abobo mai wakiltar Rally of the Republicans a shekarar 2011, mace ɗaya tilo da ta shiga gwamnati a lokacin. [1] [4] Daga nan aka zaɓe ta a matsayin shugabar hukumar kula da harkokin ƙasa da ƙasa. An naɗa ta Ministar Sadarwa a ranar 22 ga watan Nuwamba 2012, [2] kuma mataimakiyar mai magana da yawun gwamnati. [1] [5] A cikin watan Mayun 2016, ta sanar da wani tsari na 'yantar da talabijin a cikin Ivory Coast. [6]
A zaɓen 2016, Bamba-Lambine ta tsaya takarar Cocody, inda tsohuwar memba ta PDCI ta kayar da ita Yasmina Ouegnin, wacce ta sami 57% na kuri'un Bamba-Lambine 32%. [4] [7] [8] [9] Daga nan ta yi murabus a matsayin ministar sadarwa kuma Kone Bruno ya gaje ta a ranar 10 ga watan Janairu 2017.
Kyaututtuka da karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]Bamba-Lamine an sanya a matsayin jaruma na National Order na Ivory Coast a shekarar 2013. [3]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Bamba-Lamine tana da aure kuma tana da yara biyu. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 Touré, Namidja (24 November 2012). "Une dame de caractère". LeBanco (in French). Retrieved 26 January 2017.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ 2.0 2.1 Cite error: Invalid
<ref>tag; no text was provided for refs namedHDCI - ↑ 3.0 3.1 3.2 "Affoussiata Bamba" (in French). Abidjan.net. Archived from the original on 2 February 2017. Retrieved 26 January 2017.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ 4.0 4.1 "Profils comparés: Yasmina Ouegnin-Affoussiata Bamba Lamine". ICI Abidjan (in French). 12 December 2016. Archived from the original on 9 July 2019. Retrieved 26 January 2017.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ Le Guerinec, Richard (24 February 2016). "Côte d'Ivoire : la ministre Affoussiata Bamba signe " Compaoré est ivoirien. C'est tout "". Afrieque sur 7 (in French). Archived from the original on 5 October 2017. Retrieved 26 January 2017.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ Tirvengadum, Priscilla (4 March 2016). "Ivory Coast to Launch Tender for Private Commercial Television Licenses in May". Nex TV news International. Archived from the original on 9 July 2019. Retrieved 26 January 2017.
- ↑ "Législatives 2016 : Affoussiata Bamba Lamine affronte Yasmina Ouégnin, à Cocody". La Seve (in French). 18 November 2016. Archived from the original on 2 February 2017. Retrieved 26 January 2017.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ Yao, Euege (22 December 2016). "Affoussiata Bamba-Lambine: La Lutte Continue". Ma Presse Perso. Archived from the original on 9 July 2019. Retrieved 26 January 2017.
- ↑ "Affoussiata Bamba-Lamine reconnait sa défaite après s'être autoproclamée "élue"". Diaspo Ivoire (in French). 22 December 2016. Retrieved 26 January 2017.CS1 maint: unrecognized language (link)