Jump to content

Ago Are, Atisbo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ago Are wani kauyene a karamar hukumar Atisbo dake Jihar Oyo, Najeriya.[1]

Sarkin farko na kauyen Aare Olaniya ne ya kafa garin a cikin shekarar 1868.[2] Garin ya samo sunan shi ne daga lakabin sarautan gargajiya na garin Aare. A fassarar harshe, "Ago" na nufin mazauni ko birni, inda Aare ke “Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa" ma'ana Babban Kwamanda/Shugaban Yaki", ko kuma "Babban Janar na Kasar Yarbawa". Ta haka, Ago-Are na nufin "Birnin Babban Kwamandan Yaki".[2]

Labarin Kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ago-Are na nan a karkashin karamar hukumar Atisbo, Jihar Oyo, Najeriya. Tana nan a daidai lamban wuri Lattitude 8° 30' 0" N, Longitude 3° 25' 0" E. Dangane da yanayin sararin samaniya, tana karkashin Aw : Tropical savanna, wet dangane da rabe-raben yanayi na Koppen.[3]

Tana da lambobin tura sakonnin wasika kamar haka; 203105.[4]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


  1. https://www.mindat.org/feature-2351850.html
  2. 2.0 2.1 https://oyoaffairs.net/brief-history-of-ago-are/
  3. https://www.mindat.org/feature-2351850.html
  4. https://www.nigeriapostcode.com/oyo-atisbo-ago-are-owo-ago-are.html#google_vignette