Ahmed Abdullahi (gwamna)
Disamba 1987 - ga Yuli, 1988 ← Mohammed Ndatsu Umaru - Ibrahim Alkali → | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Freetown, 22 ga Augusta, 1945 (80 shekaru) | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Harshen uwa | Hausa | ||
| Karatu | |||
| Makaranta | Jami'ar Tsaron Nijeriya | ||
| Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa da minista | ||
| Digiri | Janar | ||
Birgediya Janar (mai ritaya) Ahmed Abdullahi ya kasance shugaban mulkin soji na Jihar Kwara, Najeriya tsakanin watan Disamba 1987 zuwa Yuli 1988 a lokacin mulkin soja a karkashin Janar Ibrahim Babangida. [1]
Haihuwa da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Abdullahi a Freetown, Sierra leone, a ranar 22 ga watan Agusta 1945. Ya halarci makarantun firamare a Zariya da Keffi da kuma sakandare a Freetown da Abuja. Ya samu gurbin karatu a Kwalejin Tsaro ta Najeriya, Kaduna, inda ya kammala a 1968. Daga baya ya yi karatu a British Army Royal School of Signals don Sadarwar mai sauƙi (1970 – 1971), Makarantar Sojojin Amurka ta Artillery, Oklahoma, Jihohin Amurka (1975), command and staff college, Jaji (1978), Kwalejin Ma’aikatan Marines na Amurka, Onautico, Amurka (1980 – 1981) da Kwalejin Tsaro ta Imperial.
Aikin soja
[gyara sashe | gyara masomin]An nada Abdullahi a matsayin Lieutenant a watan Yuli 1968. An nada shi a matsayi na biyun mai bada umurni sannan kuma kwamandan 2 Division Signal Regiment, Benin City. A 1973 ya zama Kwamanda, 4th division Signal Regiment. Ya kasance lakchara a Kwalejin Command and Staff College, Jaji (1982-1984). [2]
An nada Lt. Kanar Abdullahi Ministan Sadarwa (1984-1985). [2] A cikin wannan matsayin, ya taimaka a juyin mulkin watan Agusta 1985 inda Janar Ibrahim Babangida ya karbi mulki. A ranar 12 ga watan Satumba 1985 an nada shi Ministan Ci gaban Jama'a, Matasa da Wasanni, kuma ya kasance memba na Majalisar Zartarwa ta Tarayya. [3] An nada shi gwamnan soja a jihar Kwara daga watan Disamba 1987 zuwa Yuli 1988. [1] Janar Abdullahi shi ne Daraktan hukumar leken asiri na soji (DMI) kuma mai goyon bayan Janar Sani Abacha a lokacin da aka soke zaben shugaban kasa na MKO Abiola a 1993, wanda ya kai ga Sani Abacha ya karbi mulki a matsayin shugaban kasa. [4]
Lokacin Mulki
[gyara sashe | gyara masomin]An nada Lt. Kanar Ahmed Abdullahi a matsayin Gwamnan Jihar Kwara a shekarar 1986, wanda ya shahara da ayyukan samar da ruwa da kuma bunkasa noma. Abdullahi ya yi aiki tare da UNICEF, BIWATER Rural Water Supply Scheme, da kuma Directorate For Food, Roads and Rural Infrastructures (DFRRI) don samar da tsaftataccen ruwan sha ga al'ummomi a fadin jihar. Ya kuma karfafa sharar gonan noman ta hanyar gina shagunan takin zamani, cibiyoyin ayyukan noma Archived 2023-06-12 at the Wayback Machine, da tsarin tallafin tractor. Baya ga aikin da ya yi kan ruwa da noma, Abdullahi ya kuma bunkasa masana'antu da kasuwanci a jihar Kwara. Ya kafa ko tallafawa da daman kasuwanci, ciki har da Kwara Breweries, Erin-Ile Paper Converters, United Foam Limited, Gateway Insurance Company, Kwara Furniture Manufacturing Company, Kwara Hotels Limited, da kuma Trade Bank. Gwamnatin Abdullahi ta kuma bullo da wani shiri wanda ya samar da tallafin da ya dace ga al'ummomin da suka fara ayyukan hadin gwiwa a fannonin samar da wutar lantarki, ruwa, hanyoyi, da lafiya. Zaman Abdullahi a matsayin gwamna ya samu gagarumin ci gaba a fannoni da dama. Ana tunawa da shi a matsayin hazikin shugaba kuma mai nagarta wanda ya yi tasiri mai dorewa a jihar Kwara. [1] Archived 2020-09-20 at the Wayback Machine
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Lt. Kanar Abdullahi ya rasu ne a watan Fabrairun 2021, bayan gajeriyar jinya. [2] [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Nigeria States". WorldStatesmen. Archived from the original on 28 May 2010. Retrieved 2010-05-29.
- ↑ 2.0 2.1 Akintunde and Belinda Mbonu (16 August 2009). "In The News". Newswatch. Retrieved 2010-05-29.
- ↑ Max Siollun. "Babangida: His Life And Times (Part 4 )". Gamji. Archived from the original on 2011-07-11. Retrieved 2010-05-29.
- ↑ Dangiwa Abubakar Umar (March 29, 2004). "Obasanjo struck mortal blow against June 12". Sun News. Retrieved 2010-05-30.