Jump to content

Aisha Abimbola

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aisha Abimbola
Rayuwa
Haihuwa jahar Legas, 1974
Mutuwa 2018
Sana'a
Sana'a jarumi
IMDb nm2539122

Aisha Abimbola (An haife ta 19 ga watan Disamba, shekara ta 1970 - Ta mutu ranar 15 ga watan Mayu, 2018)[1] an haife ta a Epe, Jihar Legas, ta kasance 'yar fim din Najeriya kuma tauraruwar fina-finan Yarbanci.[2]

Kuruciya da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abimbola a Epe, Jihar Legas a cikin dangi musulmai amma daga baya ta juya zuwa kiristanci Kiristanci wanda ta wanzu har sauran rayuwar ta. Ta taɓa faɗa a wata hira da ta yi da New Telegraph cewa sha'war ta ga wasan kwakikwayo ya hana ta zama fasto.[3] Ta auri Victor Ibrahim Musa kuma sun haifi yara biyu.[4][5] Aisha ta halarci karatunta na sakandare a Ebute Elefun High School kuma ita ce Head girl a set din shekarar 1994.[6] Bayan haka, ta ci gaba da zuwa Kwalejin Fasaha ta Jihar Legas (LASPOTECH) inda ta samu shaidar kammala da da matsayin diploma (HND) inda ta karanta ɓangaren girke-girke da kula da hotel.[3][5]

Fina-finanta

[gyara sashe | gyara masomin]
  • No Pain
  • No Gain
  • Awerijaye
  • So Wrong So Right
  • Omoge Campus
  • Kamson and Neighbours

Lambar Yabo

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Lambar yabo na City People Entertainment Award don Jarumar fim din Yarbanci na Shekara (2015).[5]

Abimbola ta mutu daga cutarSankaran Nono a wani asibiti da ke Kanada, a lokacin tana da shekaru 47.[7][8] Tana da 'ya'ya biyu wadda babbar kawarta ta Lola Alao taci nasarar kula da su bayan ta kai tsohon mijin marigayiyar jarumar kotu kuma taci nasarar karar.[9]

  1. "Aisha Abimbola Biography". LATEST NIGERIAN NEWS BREAKING HEADLINES NEWSPAPERS (in Turanci). 2018-05-18. Retrieved 2020-11-10.
  2. "Nigerian Actress Aisha Abimbola Laid to Rest in Canada". allAfrica.com (in Turanci). 2018-05-17. Retrieved 2020-11-10.
  3. 3.0 3.1 "7 things you should know about the late Yoruba actress". Pulse Nigeria (in Turanci). 2018-05-16. Retrieved 2020-11-10.
  4. Reporter (2019-02-02). "Late AISHA ABIMBOLA's Ex-Husband Wants Custody Of The Kids". City People Magazine (in Turanci). Retrieved 2020-11-10.
  5. 5.0 5.1 5.2 Bivan, Nathaniel (2018-05-19). "Nollywood actress Aishat Abimbola has died". Daily Trust (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-10. Retrieved 2020-11-10.
  6. "Nollywood actress, Aisha Abimbola dies of breast cancer in Canada". National Pilot Newspaper (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-10. Retrieved 2020-11-10.
  7. "Actors mourn as Aisha Abimbola dies in Canada". guardian.ng. 17 May 2018. Retrieved 2020-11-10.
  8. "Aisha Abimbola 'Omoge Campus' Actress Dies in Canada". Business Post Nigeria (in Turanci). 2018-05-16. Retrieved 2020-11-10.
  9. Owolawi, Taiwo (2020-01-30). "Late Aisha Abimbola's son denies being maltreated by Lola Alao". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2020-11-10.