Akie Dagogo Fubara
| |||
| Rayuwa | |||
| Sana'a | |||
| Sana'a |
civil servant (en) | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa |
Rivers State People's Democratic Party (mul) | ||
Deacon Akie Dagogo Theodore Fubara ma'aikacin banki ne, ɗan kasuwa, ɗan siyasa kuma mai taimakon jama'a daga Opobo–Nkoro a jihar Ribas, Najeriya. Dan jam’iyyar People’s Democratic Party na jihar Ribas, ya yi aiki a matsayin kwamishinan sufuri a majalisar zartarwa ta Wike ta farko.[1]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Fubara yana da digiri na farko a fannin kimiyyar siyasa da gudanarwa da kuma digiri na girmamawa a fannin falsafa da gudanar da albarkatun ɗan adam daga Jami'ar Kirista ta Tam-Light, mai alaƙa da Jami'ar Kirista ta Indiana.[1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2006, Fubara ya tsaya takarar wakiltar mazabar Andoni – Opobo – Nkoro a majalisar wakilai ta tarayya bai yi nasara ba. Ya rike mukaman siyasa da dama da suka hada da memba na kwamitin rikon kwarya na jihar Ribas a shekarar 2007, shugaban kungiyar yakin neman zaben jihar Rivers, kodinetan yakin neman zaben karamar hukumar Opobo–Nkoro a zaben 2015 da kuma mamba a karamin kwamitin kaddamar da kula da wuraren a shekarar 2015, kafin a nada shi a matsayin kwamishinan sufuri.[1]