Al-Qadr (surah)
Al-Qadr (Larabci, "kadari, daraja") shi ne babi na 97 (sūrah) na Alkur'ani, yana da ayoyi biyar 5. Surah ne na Makka wanda ke nuni ga daren farko da aka aika wahayi na farko na abin da zai zama Alkur'ani. An sanya wa babin sunane sakamakon kalmar al-qadr a cikin aya ta farko. Suran dai yafi magana ne akan iko.
Takaitaccen Bayani
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 - Alkur'ani ko haske daga Allah da aka tabbatar wa Muhammadu a daren al Qadari
- 2-5 - Bayanin daren Al Qadari da kuma yabashi
Laylat al-Qadr
[gyara sashe | gyara masomin]
Surah na 97 ya bayyana Laylat al-Qadr, "Daren da ke cikie da dumbin albarkatu" a cikin Ramadan inda Musulmai suka yi imanin cewa a daren aka fara bayyana Alkur'ani. Wannan dare ba za a iya kwatanta shi da wasu ba a fahimtar Musulmai [1] kuma bisa ga maganar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW),albarkatun ayyukan ibadah a wannan daren ya fi bauta na tsawon rayuwan wasu. Sakamakon ayyukan ibada da aka yi a cikin wannan dare ɗaya, ya fi lada na kusan shekaru 83 (watanni 1000) na ibada. An ambaci Laylat al-Qadr a cikin Alkur'ani:
- Lallai mun aika da Alkur'ani a daren al Qadr.
- Kuma menene zai sa ka fahimci yadda dare na al Qadr yake?
- Daren al Qadr ya fi watanni dubu.
- Mala'iku da ruhu wato Jibirilu suna saukowa a daren, da izinin Ubangiji, game da kowane al'amari.
- Salama ce har zuwa fitowar alfijir.
"Ruhu" da aka ambata a aya ta 4 ana fassara shi da nufin cewa mala'ika Jibreel (Gabriel) ne. "Salama" da aka ambata a suran, Mujahid ya kira shi "tsaro wanda Shaytan (Iblis) ba zai iya yin wani mugunta ko wani lahani ba", yayin da Ibn Kathir ya nakalto maganar Ash-Sha'bi yana cewa, yana nufin mala'iku suna gaishe da mutane a cikin masallatai a cikin dare.
Daren al-Qadr yana faruwa ne a dararen witiri a cikin kwanaki goma na ƙarshen Ramadan, amma ainihin ranar ba ta da tabbas. Musulmai suna ganin cewa lokaci ne mai kyau don yin addu'a, neman tsari da kuma tuba zuwa ga Allah. Wannan lockaci yana ishara izuwa saukowar wahayi na farko na Alkur'ani zuwa Duniya. Tabattaciyar koyarwar Musulunci ita ce Muhammadu ya karbi wahayi kadan-kadan wadda suka hadu suka zama Alkur'ani a cikin shekaru ashirin da uku daga wahayin farko har zuwa lokacin mutuwarsa. Musulman Shia sun yi imanin cewa Ali (Iimamin Shia na farko, kuma Khalifa na huɗu na Shiryayun Khalifofi ga mabiya mazhabar Sunni) yana da basira ta musamman da kusanci da Allah a wannan dare.
Rubutun
[gyara sashe | gyara masomin]ِبِسْمِ ٱللهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيْم
1. إِنَّآ أَنزَلْنَٰهُ فِى لَيْلَةِ ٱلْقَدْرِ
2. وَمَآ أَدْرَٰكَ مَا لَيْلَةُ ٱلْقَدْرِ
3. لَيْلَةُ ٱلْقَدْرِ خَيْرٌ مِّنْ أَلْفِ شَهْرٍ
4. تَنَزَّلُ ٱلْمَلَٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِم مِّنْ كُلِّ أَمْرٍ
5. سَلَٰمٌ هِىَ حَتَّى مَطْلَعِ ٱلْفَجْرِ
Bayanan da aka ambata
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedOxford
Haɗin waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Alkur'ani 97 Fassarar Alkur'anFassarar Alkur'ani mai haske
- Ayyukan da suka shafiAlkur'ani Mai Tsarki (Maulana Muhammad Ali) /97. Mai Girmaa Wikisource
- Q97:1, 50+ fassarori, islamawakened.com
- Surah Qadr