Alabira Ibrahim
7 ga Janairu, 1997 - 6 ga Janairu, 2001 District: Mion Constituency (en) Election: 1996 Ghanaian general election (en) | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Mion District, | ||
| ƙasa | Ghana | ||
| Karatu | |||
| Harsuna | Turanci | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa |
People's Convention Party (en) | ||
Alabira Ibrahim ɗan siyasar ƙasar Ghana ne kuma ɗan majalisar wakilai ta biyu a jamhuriya ta huɗu mai wakiltar mazaɓar Mion a yankin Arewacin Ghana.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ibrahim ne a garin Mion dake yankin Arewacin ƙasar Ghana. Ya yi karatun lissafi a Jami'ar Cape Coast, Ghana, da Jami'ar Bristol, United Kingdom. [1] [2]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Alabira Masanin Ilimi ne kuma Mallakin Makarantar Koyar da Kwamfuta ta Sawaba da ke Tamale baya ga kasancewarsa tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Mion. [3] Shi ma ma'aikacin ci gaba ne. [4]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An fara zaɓen Ibrahim ne a matsayin ɗan majalisa a kan tikitin jam'iyyar Convention People's Party for the Mion Constituency a Arewacin Ghana a lokacin babban zaɓen Ghana na watan Disamba 1996. Ya samu kuri'u 9,519 daga cikin 20,937 masu inganci da aka kaɗa wanda ke wakiltar kashi 32.70% a kan abokin hamayyarsa Iddisah Kojo Jacob wanda ya samu kuri'u 6,198, Abu E. Musah ya samu kuri'u 5,220 da Fuseini Saaka Alidu wanda ya samu kuri'u 0. [5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Mr. Alabira Ibrahim – Policy, M & E Manager". gasip.org. Retrieved 12 October 2020.
- ↑ "Alabira I. | M&E Specialist, & Policy Research Lead | Chemonics International Inc. | Devex". www.devex.com. Retrieved 12 October 2020.
- ↑ "Ibrahim Alabira files nomination as CPP Parliamentary Candidate for Mion". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 12 October 2020.
- ↑ "Alabira Ibrahim". www.astronomerswithoutborders.org. Retrieved 12 October 2020.
- ↑ FM, Peace. "Ghana Election 1996 Results – Mion Constituency". Ghana Elections – Peace FM. Archived from the original on 8 February 2024. Retrieved 12 October 2020.