Alan Rake
Alan Rake | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1933 (90/91 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida da marubuci |
Alan Rake (an haife shi a shekara ta 1933) ɗan jarida ne a jaridar da ake bugawa da turanci, kuma marubuci game da Afirka.[1]
Farkon Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Alan Rake ya yi karatu a Jami'ar Oxford, inda ya karanci fannin: Falsafa, siyasa da tattalin arziki.[2] Jim Bailey ya gayyace shi, wanda kuma ya yi karatu a Oxford, don yin aiki da mujallar Drum.[3] A ƙarshen shekarar 1950 ya buɗe ofishin mujallar a birnin Nairobi, yana aiki a matsayin editanta jaridar ta Gabashin Afirka. A farkon 1960s ya ɗan yi aiki da mujjalar Drum a Afirka ta Kudu, kuma a matsayin Babban Manajan jaridar a Afirka ta Yamma,[4] kafin ya ci gaba da aiki da mujjalar Drum ɗin ta Gabashin Afirka a matsayin editan jaridar da ke Landan.[1]
A cikin 1968 ya kasance editan labarai na Africa Confidential a takaice.[5]
A cikin 1969 ya fara gyara a mujallar African Development da ake bugawa duk wata-wata daga Landan, daga baya aka sake mata suna izuwa New African. Ya kasance a can a matsayin edita har zuwa ritayarsa a shekarar 1999.[6]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]- (tare da John Dickie) Wanene a Afirka; shugabannin siyasa, soja da na kasuwanci na Afirka . London: Mai Saye da Kasuwanci na Afirka, 1973.
- Wanene Wane a Afirka: shugabannin 1990s . Metuchen, NJ: Scarecrow Press, 1992.
- Manyan Afirka 100 . Metuchen, NJ: Scarecrow Press, 1994.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Miranda H. Ferrara (2004). The Writers directory 2005. St. James Press. p. 1388. ISBN 978-1-55862-528-0.
- ↑ Alan Rake (2001). African Leaders: Guiding the New Millennium. Scarecrow Press. back cover. ISBN 978-0-8108-4019-5.
- ↑ Jim Bailey (1993). "Foreword". Kenya, the National Epic: From the Pages of Drum Magazine. East African Publishers. p. iv.
- ↑ "Contributors". Transition. 2 (4): 4. June 1962. JSTOR 2934806.
- ↑ "Africa Confidential: History". Retrieved 7 March 2021.
- ↑ Alan Rake (June 1999). "A Drum boy in Africa". New African. 375.