Jump to content

Alayyafo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alayyafo
Scientific classification
KingdomPlantae
OrderCaryophyllales (mul) Caryophyllales
DangiAmaranthaceae (en) Amaranthaceae
GenusAmaranthus (en) Amaranthus
jinsi Amaranthus caudatus
Linnaeus, 1753
furen alayyahu
Irin shuka alayyahu
Alayyafo
Ganyen alayyafo KO alayyahu ganyene Wanda ake miya KO DA fa abinci dashi musammanma data duka domin yana DA matuqar amfani ga lafiyar dan Adam.

Alayyahu wani koren ganye ne da ake amfani da shi a sassa daban-daban a fadin duniya wanda kowa na iya saye saboda rashin tsada ta fuskar kudi. Ya kuma samo asali ne daga dangin abinci ana kiransa da suna kamar haka: English = Spinach Hausa = Alayyahu Arabic = Sabanikh India =Paalak Yoruba =Efo yarin Igbo =kaorama Wannan ganye ya kunshi sunadaran gina jiki da inganta lafiyar dan’adam da suka hada da: niacin, zinc, protein, folate, calcium, iron, beta-carotene, luthene, danthene, chlorophynyll, magnesium, phosphorus, potassium, copper da kuma manganese.

Masana kiwon lafiya suna shawartar al’umma da su yi riko da wannan ganye a mu’amalolinsu na yau da kullum da abinci, sakamakon wannan sunadarai da ya kunsa domin inganta lafiyar jiki. Alayyahu yana inganta lafiyar dan’adam, ga kadan daga cikin su: Inganta karfin gani sakamakon sunadaran beta-carotene, luthene da danthene. Wannan sunadarai suna kuma warkar da cututtukan idanu na dan-Adam. Sunadaran folate, potassium da antiodidants dake kunshe a cikin alayyahu su kan kawar da cutar kwakwalwa. Kawar da cutar hawan jini tare da bude tashoshin da magudanan jini. Suna kuma kawar da cututtukan zuciya. Ganyen alayyahu ya kunshi sunadaran bitamin K, manganese, zinc, copper, phosphorus da kuma magnesium da suke inganta karfin kashi na jikin dan’adam. Kariya da kuma warkar da cutar gyambon ciki wato Ulcer. Sunadaran folate, tocopherol da kuma chlorophyllin su na warkar tare da bayar da kariya ga cutar daji musamman ta mama na mata da hanji na cikin dan’adam. Kare fatar dan’adam daga cututtuka. kare mutum daga rama, ganyan alayyahu yana da sinadarin da suke kare mutum daga ramewa. Kara kwarin kashi, ganyan alayyahu yana da sinadarin bitamin k wanda yake taimakawa kwayoyin halittarka wajan taimakawa kashi ya kara kwari. Yana kare mutum da kamuwa da cutar ciwan koda. Yana taimakawa jiki ya kara kyau saboda yana da sinadarin zinc. Yana taimakawa kwakwalwa wajan aiki tukuru. Yana kare fatar mutum daga illar zafin rana. Yana taimakawa gashi ya kara girma sannan ya yi kyau. Yana tace jini da kuma kara jini. Yana bada kariya ga cututtukan fuska kamar su kuraje da yaushin fuska da dai sauran su. A same shi a hada shi da ruwa kadan a mutsutstsuka a shafa fuska zai gyara fuska ya kare ta daga duk wata cuta.(Zieramaranth).JPG|thumb|furen alayyefo]] [[File:Amaranthus caudatus JdP.jpg|thumb|

Alayyafo (áláyyàfóó) (Amaranthus caudatus) shuka ne.[1]

  1. Blench, Roger (2007). Hausa names for trees and plants. Cambridge: Kay Williamson Educational Foundation.