Jump to content

Aliko Dangote

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aliko Dangote
Rayuwa
Haihuwa Kano, 10 ga Afirilu, 1957 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Yara
Ahali Sani Dangote
Karatu
Makaranta Jami'ar Al-Azhar
Government College, Birnin Kudu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa, industrialist (en) Fassara, philanthropist (en) Fassara, entrepreneur (en) Fassara, business magnate (en) Fassara da babban mai gudanarwa
Employers Dangote Group
Kyaututtuka
Mamba American Academy of Arts and Sciences (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
dangote-group.com
hoton aliko dangoto
zulfi Azad with Aliko dangote
Aliko dangote petroleum company
Sultan of Sokoto, Shehu of Borno, Emir of Kano with Aliko Dangote, Bill Gates, and U.S. Ambassador James Entwistle.
Aliko Dangote College of Nursing Sciences Bauchi
Headquarters of Dangote Cement Cameroon

Aliko DangoteAbout this soundAliko Dangote , Shahararren dan kasuwa ne kuma attajiri. An haife shi a ranar goma 10 ga watan Afrilu, a shekara ta alif dari tara da hamsin da bakwai 1957) , miladiyya. Shahararren dan kasuwa ne a ƙasa Najeriya dama Afirka baki ɗaya. Dangote shine shugaban gudanarwa (CEO)kuma wanda ya ƙirkiri shaharanren kamfanin Dangote Group, mafi girman masana'antu na sarrafa kaya daban daban a faɗin Afirka ta Yamma. Dangane da jadawalin attajiran duniya, dukiyar Ɗangote sun kai kimanin Dalar Amurka bilyan US$18.6 izuwa ranar 12 ga watan Oktoban 2022, wanda hakan ya sa ya zamo wanda yafi kowa kudi a duk faɗin Afurka, kuma wanda yafi kowa kuɗi cikin baƙaƙen fata, kuma shine na 65 acikin jerin attajiran duniya.[1][2][3]

An haifi Aliko Dangote a Kano ta Jihar Kano daga zuri'ar attajirai Hausawa kuma musulmai.[4][5][6] Mahaifiyar Ɗangote, Hajiya Mariya Sanusi Ɗantata ɗiya ce ga shahararren mai kuɗi Sanusi Ɗantata.[7] Mahaifin Ɗangote kuwa Mohammed Ɗangote, abokin kasuwancin sirikinsa ne wato Sanusi Ɗantata.[8] Ta mahaifiyarsa, Ɗangote ya kasance tattaɓa kunen Alhassan Dantata, wanda yafi kowa kuɗi a faɗin Afirka ta Yamma a lokacin rasuwarsa a alif ɗari tara da hamsin da biyar 1955.

dangote ya fara karatunsa ne daga karatun addinin a makarantar Sheikh Ali Kumasi, daga bisani kuma Capital High School, Kano.[9] A shekarar alif ɗari tara da saba'in da takwas 1978 ne ya kammala karatunsa na sakandare a Government College, Birnin Kudu.[10] Yayi karatunsa na digiri a fannin kasuwanci da gudanarwa a Jami'ar Al-Azhar, Cairo.[11][9]

Sana'ar Kasuwanci

[gyara sashe | gyara masomin]
Dangote tare da Zulfi Azad a Nijeriya

]]

An ƙirƙiri kamfanin kasuwanci na Ɗangote wato Dangote Group a shekarar alif ɗari tara da saba'in da bakwai 1977, a wannan shekarar ne kuma Ɗangote yayi ƙaura zuwa garin Lagos don ya haɓaka kamfanin.[5] Ɗangote ya samu aron kuɗi dala dubu ɗari biyar $500,000 daga wurin kawunsa don fara kasuwancin kayayyaki da suka haɗa da buhunan, siminti, da sauran kayayyakin amfanin noma kaman shinkafa da sukari.[12] A tsakanin shekarun alif ɗari tara da casa'in 1990s ne, Ɗangote ya tunkari Babban Bankin Najeriya da wata shawar cewa, zai fi arha idan bankin ta baiwa kamfaninsa na sufuri daman jigilar motocin ma'aikatansu, wanda daga bisani kuma bankin ta amince da hakan.

A yau, kamfanin Dangote Group, na daga cikin kasuwanci mafi shahara a faɗin Afurka, inda suke gudanan da harkokin kasashen waje a Benin, Ghana, Zambia da kuma Togo. Kamfanin Ɗangote Group ta matsa daga matsayin masana'antar cinikayya zuwa ƙungiyan kasuwanci mafi shahara a Najeriya, inda suke da sassa daban daban kaman sashin sarrafa sikari wato Dangote Sugar Refinery, Sashin Siminti, da kuma sashin garin fulawa wato "Dangote Flour".[13] Sashin sarrafa sukari na Dangote ta mamaye kasuwancin sukari a Najeriya, a yayinda masana'antar ke samar da kusan kaso saba'in 70 na sukari ga kamfanonin kayan sha, kamfanonin giya da kuma sauran masana'antu na kayan abinci. Kamfanin ta bawa fiye da mutum dubu sha biyar 15,000 aiki daga ko ina a fadin Yammacin Afrika.

Acikin watan Yulin dubu biyu da sha biyu 2012 ne, Dangote ya bukaci Hukumar Tashar Jirgin ruwa ta Nijeriya da ta bashi hayan wani fili da ba'a amfani da shi a Tashar Jirgi na Apapa kuma sun bashi hayan.[14] Sannan daga bisani yayi gine-gine na masana'antar sukarinsa a wurin. Itace masana'anta mafi girma a duk fadin Afirka, kuma itace ta uku a girma a duniya, inda take samar da tonn 800,000(tonnes) na sukari a duk rana. Kamfanin Dangote Group tana da masana'antun gishiri da na garin fulawa kuma kamfanin ya kasance muhimmin mai shigo da shinkafa, kifi, taliya, siminnti da kuma taki. Kamfanin tana fitar da kaya kamar su auduga, kwallon cashew, cocoa, 'ya'yan riɗi da kuma citta zuwa kasashe daban daban a fadin duniya. Har wayau, kamfanin tana da muhimman hannun jari a gidajen haya, harkokin banki, fannin sufuri, masana'antun saƙa, man fetur da kuma gas.

Acikin watan Febrerun shekarata 2022 ne, Dangote ya sanar da kammala masana'antar haɗa sassan mota ƙirar Peugeot a Najeriya bayan yayi hadin gwiwa da yayi da kamfanin Stellantis Group, asalin kamfanin Peugeot da kuma gwamnatin jihohin Kano da Kaduna. Sabon kamfanin hada motocin mai suna Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN) ta fara aiki ne da hada sassan motoci kamar Peugeot ƙirar 301, Peugeot ƙirar 5008, 3008, 508 da kuma Land Trek.[15]

Dangote ya zama biloniya na farko a Najeriya a shekara ta 2007.[16] An sanar cewa arzikin Dangote sun karu da dala biliyan $9.2 a shekara ta 2013, dangane da jadawalin Bloomberg Billionaires Index wanda hakan ta sa ya zamo mutum na talatin a arziki a duniya a lokacin, sannan wanda ya fi kowa kudi a Afurka.[17] Acikin shekara ta 2015 ne, HSBC ta sanar cewa Dangote ya kasance abokin kasuwancinta kuma yana da hannun jari a yankin aminci na British Virgin Islands.[18][19] Ya zuwa watan Yunin 2022, Dangote ya kasance wanda yafi kowa kudi a fadin Afurka tare da kiyasi na dukiya akalla biliyan US$20.[1][2] Sannan shahararren ɗan Kasuwan yayi ta yunƙurin buɗe kamfanin sarrafa mai da yafi kowanne girma a Afrika ɗangote refinery, yayin da Shugaba Buhari ya ƙarfafamasa gwiwa wajen bude kamfanin a ashirin da biyar 25 ga watan Mayu na shekarar dubu biyu da ashirin da uku.

Matatar Mai Na Aliko Dangote

[gyara sashe | gyara masomin]

Matatar Dangote matatar mai ce mallakin Aliko Dangote da aka kaddamar a ranar 22 ga watan Mayun 2023 a Lekki, Najeriya.[20]

Idan aka kammala aikin, ana sa ran za ta iya sarrafa gangar danyen mai kusan ganga 650,000 a kowace rana, wanda zai zama matatar mai mafi girman aiki a duniya.

Daga farkon da aka yi kiyasin kashe dala biliyan tara 9, jimlar kudin gina matatar man dangote ya ninka dala biliyan 18.5, saboda karin tsada da dala tayi a Nijeriya.

  1. 1.0 1.1 "Aliko Dangote". Forbes.
  2. 2.0 2.1 "Dangote visits revamped Moshood Abiola Stadium -". thenationonlineng.net. Retrieved 26 February2022.
  3. "Bloomberg Billionaires Index". Bloomberg.com. Retrieved 10 June 2022.
  4. Ilan Bijaoui (2017). Multinational Interest & Development in Africa: Establishing a People's Economy. Springer. p. 55. ISBN 978-3-319-48914-8.
  5. 5.0 5.1 Gabriel Edigheji. The Entrepreneur Magazine. Lulu.com. ISBN 978-1-105-90932-0. [self-published source]
  6. "Nweke, Ifeanyi. "What you should know about Dangote". Retrieved 14 July 2015.
  7. admin (10 April 2017). "Aliko Dangote: The African Icon at 60!". THISDAYLIVE. Retrieved 6 March2022.
  8. "What you should know about Dangote - The Nation Newspaper". 23 November 2012. Retrieved 12 May 2022.
  9. 9.0 9.1 "Aliko Dangote: Things You Never Knew About Him, His Wives and Children – Naija News". naijanews.com. 17 March 2017. Archived from the original on 8 October 2017. Retrieved 8 October 2017.
  10. IV, Editorial (4 January 2018). "Birnin Kudu College hails Dangote on projects". Blueprint. Retrieved 15 March 2020.
  11. "The World's Billionaires: Aliko Dangote". Forbes.com. Retrieved 9 March 2018.
  12. `Umoh, Ruth (5 December 2018). "Billionaire Aliko Dangote is the world's richest black person—here's how he made his wealth". CNBC. Retrieved 12 May2022.
  13. "Somalia orders top U.N. official to leave". Reuters. 2 January 2019. Archived from the original on 3 January 2019. Retrieved 2 January 2019.
  14. "Dangote Sugar Refinery Plc (DSR)", Institute of Developing Economies-Japan External Trade Organization. Accessed 26 November 2015.
  15. "Africa's Richest Man, Dangote Ventures Into Automobiles". Investors King. 4 February 2022. Retrieved 7 February 2022.
  16. "Aliko Dangote, Nigeria's first billionaire cements his fortune - CNN.com". edition.cnn.com. Retrieved 12 May 2022.
  17. "Aliko Dangote Racks in $9.2 bn in 2013". BellaNaija. 3 January 2014.
  18. "Exposed: The Africans named in the HSBC Swiss Leaks". The Mail & Guardian. 13 February 2015. Retrieved 27 February 2022.
  19. "INVESTIGATION: David Mark's wife, Dangote, Adenuga, others named in #SwissLeaks as operators of secret foreign accounts | Premium Times Nigeria". 19 February 2015. Retrieved 27 February2022.
  20. Kaddamar da matatar man Dangote a Nijeriya. https://www.icirnigeria.org/economic-challenges-jack-up-dangote-refinerys-construction-cost-100/#:~:text=FROM%20its%20initial%20estimated%20cost,relations%20with%20the%20global%20economy.