Jump to content

Aliyu Jauro

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aliyu Jauro
Rayuwa
Sana'a


Aliyu Jauro (an haife shi 27 ga Yuni, 1971) ɗan Najeriya ne kuma masanin kimiyyar muhalli kuma farfesa. A ranar 26 ga watan Fabrairun 2019 ne Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin Darakta Janar kuma Shugaban Hukumar Kula da Muhalli ta Kasa (NESREA). A watan Fabrairun 2023 ne Shugaba Buhari ya sake nada shi a karo na biyu kafin Bola Tinubu ya sallame shi a watan Afrilun 2024. [1]

Aliyu Jauro ya halarci Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda ya yi digirinsa na farko a fannin kimiyar masana’antu a shekarar 1995. Ya yi digiri na biyu da na uku a fannin kimiyar masana’antu a jami’a a shekarar 1997 da shekara ta 2005.

Bayan kammala karatunsa na farko, an nada Aliyu malami a ABTU . Ya zama cikakken farfesa a shekarar 2014. A shekarar 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin DG/CEO na Hukumar Kula da Muhalli ta Kasa . A karshen wa’adinsa a watan Fabrairun 2023, an sake nada shi karo na biyu na shekaru hudu. Shugaban kasa Bola Tinubu ya soke nadin nasa bayan shekara guda a watan Afrilun 2024, inda Dr.Innocent Barikor ya maye gurbinsa.

Kyaututtuka da karramawa

[gyara sashe | gyara masomin]

a 2020, Farfesa Aliyu ya sami lambar yabo ta Nigerian National Legacy Awards. Aliyu ya lashe lambar yabo ta ma'aikatan gwamnati don fasahar muhalli a shekarar 2023 da ofishin sake fasalin ma'aikata ya yi .