Alum Sandra Ogwang Santa
|
| |||
2016 - - Beatrice Amongi Lagada (mul) | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa |
Oyam District (en) | ||
| ƙasa | Uganda | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
Ikwera Girls Secondary School (en) Jami'ar Makerere Anai Primary School (en) | ||
| Harsuna | Turanci | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a |
social scientist (en) | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | Majalisar Jama'ar Uganda | ||
Alum Sandra Ogwang (an Haife ta a ranar 2 ga watan Disamba 1972) masaniya ce a fannin ilimin zamantakewa 'yar ƙasar Uganda, 'yar siyasa kuma 'yar majalisa. [1] Ta wakilci al'ummar gundumar Oyam a matsayin wakiliyar mata a majalisar dokokin Uganda. [2] Ita mamba ce ta jam'iyyar Uganda People's Congress (UPC),[2] jam'iyya a ƙarƙashin shugabancin Jimmy Akena, wanda shi ne ɗan majalisa na gundumar Lira [3] kuma ɗan tsohon shugaban ƙasa Apollo Milton Obote.[4]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Alum ta fara karatun firamare ne a makarantar firamare ta Anai inda ta yi jarrabawar kammala firamare (PLE) a shekarar 1987. Daga nan ta shiga makarantar sakandaren ‘yan mata ta Ikwera don samun iliminta na O’level inda ta kammala shaidar karatun ta na Uganda (UCE) a shekarar 1990. Daga nan ta shiga babbar sakandire ta Bombo don karatunta na A'level inda ta kammala karatunta na Uganda Advanced Certificate of Education (UACE) a shekarar 1994. Ta halarci Jami'ar Makerere inda ta kammala karatun digiri na farko a fannin karatu da kimiyyar bayanai a shekarar 1998. Daga baya ta kara digiri na biyu a fannin ilimin jinsi a shekarar 2010 daga wannan jami'a. [2]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Alum tana aiki a matsayin darekta/ sakatariya na Sysplus Limited daga shekarun 1998 zuwa yau. [2] Daga shekarun 2005 zuwa 2006 ta kasance mai shiga bayanai a Jami'ar Makerere [2] Ta kasance mamba a kwamitin asusun jama'a na gundumar Oyam daga shekarun 2006 zuwa 2010. [2] A cikin shekarar 1998 ta kasance malama a Kwalejin Almond, Lira. [2]
Ita ce 'yar majalisar dokokin Uganda daga shekarun 2011 zuwa yanzu. [5] A majalisa ita ce bulaliya ta jam'iyyar People's Congress (UPC) na Uganda [6] kuma tana aiki a kwamitin kasuwanci da kwamitin noma. Ita ma memba ce a kungiyar 'yan majalisar dokokin Uganda (UWOPA). [7]
Alum Santa memba ce a zauren Majalisar Dokokin Uganda kan Kariyar Jama'a (UPFSP) taron da ke fafutukar kare al'umma musamman ma mafiya rauni na al'ummar Uganda. [8]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Majalisar Uganda
- Jerin sunayen 'yan majalisar dokokin Uganda na tara
- Jerin sunayen 'yan majalisar dokoki na goma na Uganda
- Gundumar Oyam
- Charles Okello Engola
- Ongom Midi Betty
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Alum Sandra Ogwang Santa". www.wikidata.org (in Turanci). Retrieved 30 May 2020.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 2.6 "Parliament of Uganda members of the 10th parliament". Parliament of uganda. Archived from the original on 27 April 2021. Retrieved 15 April 2020.
- ↑ Julius, Kitone. "Jimmy Akena seeks new term as UPC president". Nile post. Retrieved 15 April 2020.
- ↑ "Today in history: Obote becomes president". New vision. 4 March 2020. Retrieved 15 April 2020.
- ↑ "Members of parliament information". Parliament of Uganda. Archived from the original on 6 April 2020. Retrieved 15 April 2020.
- ↑ Olive, Eyotaru (1 October 2016). "Role of government chief whip questioned". Uganda radio network. Retrieved 15 April 2020.
- ↑ "Members of UWOPA 10th parliament". UGANDA WOMEN PARLIAMENTARY ASSOCIATION. Archived from the original on 18 April 2021. Retrieved 15 April 2020.
- ↑ "Our people". Uganda parliamentary forum on social protection. Archived from the original on 15 October 2022. Retrieved 15 April 2020.