Ama Hemmah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ama Hemmah
Rayuwa
Haihuwa 1938
ƙasa Ghana
Mutuwa Tema, 2010
Yanayin mutuwa kisan kai
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a

Ama Hemmah (1947-2010) wata 'yar kasar Ghana ce da aka kona da ranta saboda zargin ta da ake yi da cewa mayya ce a Tema, Ghana. Wadanda ake zargin sun yi ikirarin man zaitun da aka yi amfani da shi a kokarin fitar da mugun ruhun shine abin da ya kama wuta.[1]

Kisa[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 20 ga Nuwamban 2010 a Tema Site 15, mutane biyar sun azabtar da Hemmah wanda ke zargin ta mayya ce har sai ta furta musu. Kafin azabtar da ita, Mary Sagoe ta kama Hemmah zaune a ɗakin 'yar uwarsa Emelia bayan ta tura yaranta makaranta. An ji kararrawa wanda ya dauki hankulan wadanda suka aikata laifin, Samuel Ghunney, mai daukar hoto mai shekaru 50, Fasto Samuel Fletcher Sagoe, 55, da Emelia Opoku, 37, Nancy Nana Ama Akrofie, 46, da Mary Sagoe, 52, duk marasa aikin yi. Sun shayar da ita kananzir sannan daga baya suka cinna mata wuta.[2]

Wata daliba mai aikin jinya ce ta kawo mata dauki inda ta aike ta zuwa ofishin 'yan sanda na daya. An tura Hemmah babban asibitin Tema, inda ta mutu washegari.[3][4]

Binciken 'yan sanda[gyara sashe | gyara masomin]

Wadanda ake zargin, fasto da mai daukar hoto, sun musanta zargin a cikin bayanin da suka yi wa ‘yan sanda. An kama mutane shida dangane da lamarin, biyu daga cikinsu ana tuhumarsu da kisan kai yayin da aka saki sauran hudu akan beli yayin da suke jiran shari'a.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Shock over Ghana 'witch killing'" (in Turanci). 2010-11-26. Retrieved 2019-10-02.
  2. 2.0 2.1 "'Devil' grandma burned alive by exorcists". www.dailytelegraph.com.au (in Turanci). 2010-11-29. Retrieved 2019-10-02.
  3. Smith, David (2010-11-29). "Ghanaian woman burned to death for being a 'witch'". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Retrieved 2019-10-02.
  4. ""My mum is not a witch" | General News 2010-11-29". www.ghanaweb.com (in Turanci). Archived from the original on 2019-10-02. Retrieved 2019-10-02.