Mahamadou Amadou Sabo (an haife shi aranar 30 ga Satan Mayun shekara ta 2000) a Nijar dan kwallo ne wanda a halin yanzu yake taka leda a matsayin dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Club din Africain .
An fara kiransa zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Nijar a watan Nuwamba na shekarata 2019, amma ya cigaba da zama a kan benci. Ya fara buga wa tawagar wasa a ranar 5 ga Yunin shekarata 2021 a wasan sada zumunci da kasar Gambia.