Anambra ta Gabas
Anambra Gabas | |
|---|---|
![]() Taswirar hulɗa ta Gabashin Anambra | |
| Hanyar daidaitawa: 6°20′08′′N 6°51′46′′E / 6.3356799°N 6.86283945°E / 6.6356799; 6.86283745 | |
| Kasar | |
| Jiha | Jihar Anambra |
| Gwamnati | |
| • Irin wannan | Karamar Hukumar |
| • Shugaban Karamar Hukumar | Ifeanyi Chiweze [1] |
| Yankin | |
• Jimillar |
616.4 km2 (238.0 sq mi) |
| Yawan jama'a (2022) [2] (2022)[2] | |
• Jimillar |
659,380 |
| • Ƙarƙashin jama'a | 1,070/km2 (2,771/sq mi) |
| Yankin lokaci | UTC+1 (WAT) |
Anambra ta Gabas wata Ƙaramar Hukuma ce da ke Anambra State, a yankin tsakiyar kudancin Nigeria.[3] Hedikwatarta tana garin Otuocha.[3]
Garuruwan da suka haɗa Ƙaramar Hukumar sun haɗa da: Aguleri, Enugwu Aguleri, Eziagulu Otu Aguleri, Enugwu Otu Aguleri, Mkpunando-Otu Aguleri, Ikem Ivite, Igbariam, Umuoba Anam, Nando, Umueri, da Nsugbe.[4] Yankin na daga cikin Babban Birnin Onitsha (Greater Onitsha Metropolis). Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas tana ƙarƙashin mazabar sanatoci ta Anambra ta Tsakiya a Jihar Anambra.[5] Bisa ƙidayar jama’a ta shekarar 2006, jimillar mutanen yankin ta kai 152,149.[6]
A Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas, an gano dimbin albarkatun man fetur da iskar gas a bakin garin Aguleri. Shugaban ƙasa ya ƙaddamar da aikin bincike da haƙar man a yankin, kuma kamfanin 'Orient Petroleum Resources' na shirin kafa babban ofishinsa na gudanarwa tare da wani sabon rukunin gidaje a garin Aguleri.
A halin yanzu, Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas ta kafa tarihi bayan jirgin sama kirar '''Embraer ERJ 145''' na kamfanin Air Peace ya samu nasarar sauka da kuma tashi daga yankin. Haka kuma, gwamnatin Anambra State ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna mai darajar dala biliyan biyu tare da kamfanonin '''Orient Petroleum Resources''' da '''Elite International Investment Limited''' domin gina wani birnin filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa a Umueri da ke Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas.[7][8]
Tattalin Arziki
[gyara sashe | gyara masomin]Doya, shinkafa, rogo da ƙocoyam su ne manyan amfanin gonar da ake nomawa a Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas, wadda ta shahara a fannonin noma da kasuwanci. Kasuwanni irin su Kasuwar Otuocha, New Parts Market da Kasuwar Afia Ama suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin yankin. Baya ga noma da kasuwanci, Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas tana kuma da yalwar albarkatun ma’adinai, musamman bayan gano dimbin ɗanyen mai a garin Aguleri.[9]
Yanayi
[gyara sashe | gyara masomin]Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas na da matsakaicin zafin jiki da ya kai digiri 27.5 a ma’aunin Celsius (81.5 °F), tare da matsakaicin danshin iska na kashi 79 cikin 100. Yankin na da manyan yanayi biyu, wato lokacin rani wanda ke gudana daga watan Nuwamba zuwa Maris, da kuma lokacin damina wanda yake daga watan Afrilu zuwa Oktoba.[10]
Shahararrun mutane a Anambra ta Gabas
[gyara sashe | gyara masomin]- Willie Obiano[11]
- Tony Nwoye
- Emeka Idu
- HRM Igwe Benneth Izuchukwu Emeka
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "List Of Local Government Areas In Anambra State, And Their Chairmen". 27 September 2024.
- ↑ "Anambra State: Subdivision".
- 1 2 "List of Local Government Areas in Anambra State with Headquarters". Xplorer.ng (in Turanci). 2024-11-09. Archived from the original on 2025-12-16. Retrieved 2025-06-30.
- ↑ "Local Government Area & Towns". Anambra State Government. Archived from the original on 2021-10-17. Retrieved 2026-05-29.
- ↑ "Anambra Senatorial Districts". Centre for Community and Rural Development (in Turanci). Archived from the original on 2026-05-27. Retrieved 2025-06-26.
- ↑ "Nigeria: Administrative Division (States and Local Government Areas) - Population Statistics, Charts and Map". www.citypopulation.de. Retrieved 2025-06-30.
- ↑ "Anambra East local government area – Channels Television". Retrieved 3 March 2022.
- ↑ "Obiano Signs Two Billion Dollars Airport City MoU". Channels Television. Retrieved 25 November 2022.
- ↑ "Anambra East Local Government Area". www.manpower.com.ng. Retrieved 5 October 2023.
- ↑ "Anambra East Local Government Area". www.manpower.com.ng. Retrieved 2023-10-04.
- ↑ "Anambra State Governor". www.nggovernorsforum.org. Archived from the original on 14 March 2026. Retrieved 24 February 2023.
