Anna Ebaju Adeke
|
| |||
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Uganda, 27 Nuwamba, 1991 (34 shekaru) | ||
| ƙasa | Uganda | ||
| Mazauni | Kampala | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
Law Development Centre (en) Jami'ar Makerere | ||
| Harsuna | Turanci | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa da lauya | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa |
independent politician (en) | ||
Anna Ebaju Adeke (an haife ta 27 Nuwamba 1991) lauya ce kuma 'yar siyasa. A halin yanzu tana aiki a matsayin 'yar majalisa mai wakiltar mata a gundumar Soroti a majalisa ta 11 (2021-2026). [1] [2] Ta taɓa zama wakiliyar majalisar wakilai ta mazaɓar mata ta ƙasa a majalisa ta 10 (2016-2021). [3] [4] [5] Tana aiki a matsayin mataimakiyar shugabar dandalin sauyin Dimokraɗiyya a yankin Gabas. [6]
Tarihi da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Adeke ta halarci makarantar Our Lady of Good Counsel Gayaza a matsayin O' Level daga baya St Marys SS Kitende a matsayin A' Level. [7] Tana da digiri na farko a fannin shari'a daga Jami'ar Makerere da Difloma ta Digiri a fannin Shari'a daga Cibiyar Bunƙasa Shari'a. [2] [7] A ranar 17 ga watan Mayu 2021, Adeke ta kammala karatun digiri na biyu a fannin shari'a daga Jami'ar Makerere, a ranar da aka rantsar da ita a matsayin mamba a Majalisar Dokokin Uganda ta 11 (2021-2026). [8]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Daga shekarun 2013 zuwa 2014, Adeke ta yi aiki a matsayin shugabar Guild na Jami'ar Makerere, ta tsaya takara kuma ta yi nasara a ƙarƙashin jam'iyyar adawa ta Forum for Democratic Change. [9] Tun a shekarar 2015, lokacin da ta kammala karatun shari'a, an shigar da ita Bar a Uganda. Tana aiki a matsayin mai ba da shawara a M&K Advocates, a Kampala. [10]
A watan Maris na shekarar 2016, an zaɓi Adeke a matsayin sabuwar 'yar majalisar Matasa ta ƙasa a zaɓen ƙasa da aka gudanar a birnin Hoima na yammacin Uganda. A zaɓen ƙasar, ta yi takara a matsayin mai cin gashin kanta. [3] A matsayinta na 'yar majalisa, ta ba da shawarar raba ma'aikatar jinsi, kwadago, matasa da ci gaban zamantakewa, don ƙirƙirar ma'aikatar matasa mai zaman kanta. Ta kuma yi kamfen don ƙara yawan kuɗi ga majalisun matasa na ƙananan hukumomi, yanki da na ƙasa. [3] Ta kasance mamba a kwamitin majalisar dokoki kan tattalin arzikin ƙasa, a majalisa ta 10. [7]
A shekarar 2019, an zaɓi Adeke a matsayin shugabar majalisar dokokin Uganda kan harkokin matasa. [10] Ta kuma yi aiki a matsayin ministar harkokin matasa da yara a inuwa, kuma memba a kungiyar mata ta Uganda (UWOPA), a majalisar wakilai ta 10 (2016 - 2021). [7]
Sauran ayyukan
[gyara sashe | gyara masomin]Adeke ta bayyana a cikin Vogue Italia a watan Satumba na 2017.[11] A cikin watan Maris 2017, Mujallar Ugandan ta lissafa ta a cikin "Mata 10 Mafi Karfi A Siyasar Uganda a shekarar 2017.[12] Ita 'yar Katolika ce. [11] Har ila yau, tana da sha'awar batutuwan jinsi da na mata [13] [14] kuma ta yi Allah wadai da cin zarafi, [15] [14] [16] kuma ta yi kira ga mata da jama'a su yi magana game da mummuna na cin zarafi na jima'i da kuma yaki da shi. [17] Ta kuma yi magana a lokacin da wata 'yar majalisa ta yi kokarin lalata da ita yayin da ta tafi wata ƙasar waje. [18] [19] [20]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Kampala Post (11 June 2019). "Anna Adeke to Battle Osegge for Soroti Woman Seat in Heated 2021 Race". Kampala Post. Retrieved 7 August 2021.
- ↑ 2.0 2.1 David Mujuni (20 January 2021). "Former Makerere Guild President Adeke Anna Ebaju Wins Soroti Woman MP Seat". Campusbee Uganda. Kampala, Uganda. Retrieved 7 August 2021.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 Francis Mugerwa (7 March 2016). "Adeke is new national female youth MP". Daily Monitor. Retrieved 7 August 2021.
- ↑ IYLA (March 2016). "Hon. Anna Adeke Ebaju, National Female Youth Member of Parliament". International Young Leaders Assembly (IYLA). Archived from the original on 20 November 2018. Retrieved 8 November 2017.
- ↑ Patricia Lindrio (1 February 2017). "Ugandan Women Often Avoid Political Posts, But One 25-Year-Old Arises as a Superstar". Global Press Journal. Retrieved 7 August 2021.
- ↑ Segawa, Nixon (13 September 2021). "Lukwago, Adeke Swear in to Serve as FDC Deputy Presidents". softpower.ug. Retrieved 13 September 2021.
- ↑ 7.0 7.1 7.2 7.3 POUG (7 November 2017). "Parliament of Uganda Members Of The 10th Parliament: Adeke Anna Ebaju". Parliament of Uganda (POUG). Kampala. Archived from the original on 20 November 2018. Retrieved 7 November 2017.
- ↑ Daily Monitor & Uganda Radio Network (17 May 2021). "Double win for sworn-in MP Adeke as she graduates with Master's Degree in Law". Daily Monitor. Kampala, Uganda. Retrieved 7 August 2021.
- ↑ John Sserwaniko and Hope Muhairwe (March 2013). "Why Makerere Picked Adeke For President". Red Pepper. Archived from the original on 17 October 2022. Retrieved 7 August 2021.
- ↑ 10.0 10.1 Dickens H Okello (2 January 2019). "Anna Adeke Elected Chairperson Parliament Youth Forum". ChimpReports.com. Retrieved 7 August 2021.
- ↑ 11.0 11.1 Reyes, Jovanna (12 September 2016). "Adeke Anna Ebaju: Model and Member of Parliament". Milan: Vogue Italia. Archived from the original on 23 January 2025. Retrieved 8 November 2017. Cite magazine requires
|magazine=(help) - ↑ The Ugandan (8 March 2017). "List Of The 10 Most Powerful Women in Ugandan Politics Today". Kampala: Theugandan.com.ug (The Ugandan). Retrieved 8 November 2017. Cite magazine requires
|magazine=(help) - ↑ africanfeminism (2018-07-11). "WOMEN AND TAX- By Hon. Adeke Anna Ebaju". African Feminism (AF) (in Turanci). Retrieved 2021-04-01.
- ↑ 14.0 14.1 murami (2020-01-16). "MPs endorse campaign against sexual harassment". www.parliament.go.ug (in Turanci). Retrieved 2021-04-01.
- ↑ Ssali, Godfrey (2018-04-14). "Uganda Parliament to probe sexual abuse in schools". The Independent Uganda (in Turanci). Retrieved 2021-04-01.
- ↑ "UPFYA chairperson leads group of women activists to petition Rt. Hon. Speaker Rebecca Kadaga on sexual harassment at the workplace". UPFYA (in Turanci). 2019-05-23. Retrieved 2021-04-01.[permanent dead link]
- ↑ Nakatudde, Olive. "Parliament Committee to Investigate Sexual Abuse in Schools". Uganda Radio Network (in Turanci). Retrieved 2021-04-01.
- ↑ "MP Anna Adeke Accuses Male Colleague of Sexual Harassment on Trip". Vanguard News (in Turanci). 2021-03-10. Retrieved 2021-04-01.
- ↑ "MP Adeke claims colleague sexually harassed her on trip". Daily Monitor (in Turanci). 10 March 2021. Archived from the original on 2021-03-18. Retrieved 2021-04-01.
- ↑ "Soroti MP Adeke Raises Claims of Sexual Harassment from Fellow MP". Daily Express News (in Turanci). 2021-03-10. Retrieved 2021-04-01.