Anne Gnahouret Tatret
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | 20 century |
| ƙasa | Ivory Coast |
| Karatu | |
| Harsuna | Faransanci |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa, Mai wanzar da zaman lafiya da minista |
| Imani | |
| Jam'iyar siyasa |
Mouvement des Générations Capables (en) |
Anne Gnahuret Tatret ta kasance 'yar siyasa ce ta ƙasar Ivory Coast. Yayin da ta kammala karatun shari'a a shekarar 1978, Gnahuret ta zama shugabar sashen shari'a na tashar jiragen ruwa mai cin gashin kanta ta San-Pedro.[1] Ta yi aiki a can har zuwa shekara ta 2000, kuma tana neman aikin siyasa. Ta shiga jam'iyyar Popular Front (FPI) a ƙarƙashin jagorancin Emile Boga Doudou. Daga shekarar 2002, ta yi aiki a matsayin jami'ar diflomasiyya, inda ta kasance jakadiyar Ivory Coast a Angola, Mexico da Cuba. [1] An saka ta a cikin jerin sunayen 'yan siyasar Ivory Coast a shekarar 2011 wanda Tarayyar Turai ta ƙaƙabawa takunkumi.[2]
A cikin shekarar 2019, gabanin zaɓen shugaban ƙasar Ivory Coast na shekarar 2020, Pascal Affi N'Guessan ta naɗa mataimakiyar a Sashen Lakota na gundumar Lôh-Djiboua.[3] Bayan zaɓukan, Gnahuret ta zama shugabar kungiyar mata ta 'yan Ivory Coast Popular Front (OFFPI). Ta tallafa wa Angélique Kili, matar N'Guessan, lokacin da aka kama shi na dare ɗaya.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 DJANGONÉ, Ange-Stéphanie (12 December 2019). "Anne Gnahouret Tatret, Nouvelle amazone du FPI". Journal d'Abidjan (in Faransanci). Retrieved 21 December 2022.
- ↑ "Sanctions de l'Union Européenne - La liste des 85 personnalités et 11 entités ivoiriennes sanctionnées - Abidjan.net News". Abidjan net (in Faransanci). 17 January 2011. Retrieved 21 December 2022.
- ↑ Kouassi, Jean Kelly (20 August 2019). "Côte d'Ivoire: Vaste mouvement au sein du FPI d' Affi N'guessan". Afrique-sur7 (in Faransanci). Retrieved 21 December 2022.
- ↑ KOFFI, Parfait (18 November 2020). "L'Organisation des femmes du front populaire ivoirienne (Offpi) rend visite à Angélique Kili, épouse d'Affi n'Guessan". L'infodrome (in Faransanci). Retrieved 21 December 2022.